Garkuwa da mutane: Hanyar Kaduna zuwa Abuja ta gyaru yanzu - IG Adamu ga matafiya

Garkuwa da mutane: Hanyar Kaduna zuwa Abuja ta gyaru yanzu - IG Adamu ga matafiya

An samu galaba akan masu garkuwa da mutane a hanyar kaduna zuwa Abuja,yanzu hanyar ta gyaru ma matafiya, cewar mukaddashin sifeton yan sanda, Mohammed Adamu.

Adamu ya bayyana hakane a wani taro da akayi a fadar shugaban kasa tsakanin shugaban kasa buhari da shugabannin hukumomin tsaro da wasu manyan hukumomin tsaro a Abuja ranar alhamis.

Shugaban yan sandan yace an kama da yawa daga cikin masu garkuwa da mutane wasu kuma sunji raunuka a yayin da suka yi kicibis dasu a wani aiki na musamman na yankin da abin ya shafa.

Yace: "Ina mai tabbatar ma yan Nigeria cewa hanyar kaduna zuwa Abuja ta gyaru yanzu,..mun kama masu garkuwa da mutane da yawa wasu kuma sun ji raunuka masu tsanina yayinda muka yi gaba da gaba da su."

“Yanzu matafiya da yan sandanmu zasu iya bin hanyar da jamian tsaro wanda zasu rika aiki na awa 24."

Shugaban hukumar tsaro, Janar Gabriel Olonishakin, yayi tsokaci a karshen taron inda yake cewa shugaba Buhari ya umurci jami’an tsaro dasu gaggauta samo maslaha akan barandanci da matsalolin tsaro da suke addaban wasu daga cikin garuruwan kasar.

Yace: "Umarnine aka bamu na kai tsaye da mu samo maslaha akan barandanci da kuma wasu matsalolin tsaro da suke damun kasa.”

NAN ta bada rahoto cewa a ranar 5 ga watan Aprilu, Adamu ya kaddamar da atisayen ”Puff-Ader” domin dakile masu garkuwa da mutane, masu barandanci da sauran harkokin ta’addanci a hanyar Abuja zuwa kaduna.

Atisayen ya hada da hanyar Abuja zuwa kaduna da wasu kauyuka zuwa jihar Kogi, Katsina, Niger, da Zamfara.

Atisayen wanda da hadakar sojojin Nigeria da DSS,s un samar da wanda suka kware akan kyakyawun tsaro da isassun makamai da wanda suka jajirce akan aiki tare da hadakar kayan ayyuka daga kowanni sashi na jami’an tsaro.

KU KARANTA: Kungiyar kwadago ta bawa Okorocha sati daya ya biya ma'aikatan jihar albashin da suke binshi

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel