Dole ka yi magana a kan matsalar Zamfara, mun ba ka sa'a 48 - 'Yan majalisa ga Buhari

Dole ka yi magana a kan matsalar Zamfara, mun ba ka sa'a 48 - 'Yan majalisa ga Buhari

Majalisar wakilai ta bawa shugaban kasa Muahammadu Buhari wa'adin sa'a 48 ya gabatar da jawabi ga 'yan Najeriya a kan irin shirin da ya ke da shi wajen kawo karshen 'yan ta'addar da ke kashe mutane a fadin kasar nan.

'Yan majalisar sun amince da kafa wani kwamiti da zai tunkari fadar shugaban kasa, ministan tsaro, shugabannin rundunonin tsaro, shugaban rundunar 'yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki, domin samun mafita daga kashe-kashen da 'yan bindiga, makiyaya da sauran 'yan ta'dda ke yi ba dare ba rana a fadin kasar nan.

Majalisar ta yanke wannan shawara ne biyo bayan wasu kudiri masu bukatar kulawar gaggawa a kan kashe-kashen 'yan bindiga da makiyaya, wanda Mark Gbillah (dan jam'iyyar APC daga jihar Benuwe) ya gabatar da na bukatar bincike a kan kisan Dakta Ferry Gberegbe da ake zargin jami'an 'yan sanda da aikata wa, wanda Kenneth Chinda (dan jam'iyyar PDP daga jihar Ribas) ya gabatar.

Dole ka yi magana a kan matsalar Zamfara, mun ba ka sa'a 48 - 'Yan majalisa ga Buhari

Majalisar wakilai
Source: Twitter

Mambobin majalisar sun ce ba zasu yarda ko su zuba ido ana kashe 'yan Najeriya ba, ba tare da sun yi wani abu a kan hakan ba.

DUBA WANNAN: Rashin kwazo: IGP zai saka wa kwamishinonin 'yan sanda na jihohi takunkumi

"Mu na son shugaban kasa, a matsayinsa na shugaban hukumomin tsaro, ya fito cikin sa'a 48 domin yiwa 'yan Najeriya jawabi a kan irin matakan gaggawa da zai dauka domin tunkarar 'ayn ta'adda a duk inda su ke tare da kwar da su.

"Idan har shugaban kasa ya ki yin hakan kamar yadda muka bukata, zamu shiga cikin 'yan Najeriya da ke cewa gwamnatinsa ba za ta iya dakatar da kisan kiyashi da ake yiwa 'yan Najeriya ba," a cewar kudirin Gbillah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel