Yan bindiga sun kwace sassan jihar Katsina - Aminu Bello Masari

Yan bindiga sun kwace sassan jihar Katsina - Aminu Bello Masari

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyanawa sifeto janar na yan sanda, Muhammad Adamu da duniya cewa yan bindiga da garkuwa da mutane sun kwace wasu sassan jihar daga hannunsa.

Ya laburta hakan ne ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, 2019 inda yake cewa wasu kananan hukumomin jihar dake daura da jihar Zamfara da abin ya shafa.

Gwamnan wanda yayi magana ta bakin mataimakinsa, Mannir Yakubu, ya ce: "Wadannan yan barandan sukan kai hari lokacin da suka ga dama, su hallaka mutane, su lalata dukiyoyin jama'a yadda suka ga dama."

KU KARANTA: Yaki da masu satar mutane: An damke yan bindiga 46, an kashe 10 - Sifeto Janar

"A wasu sassan wannan jihar, muna da masu satar mutane da ta'addancinsu ya tashi daga tare hanya, yanzu gidajen mutane suke shiga suke sace mutane. Irin wannan ya faru da surukar gwamna wacce aka sace cikin gidanta."

Kawo yanzu, gwamnatin jihar ta gana da shugabannin kananan hukumomi takwas da wannan matsala ya shafa yankunansu kan abinda za'a iya yi na kawo karshen yan baranda da masu garkuwa da mutane.

Kananan hukumomin da abin ya shafa sune Jibia, Batsari, Safana, Dan-Musa, Faskari, Sabuwa, Dandume da Kankara. Yawancin wadannan kananan hukumomin na daura da jihar Zamfara.

A wani labari mai kama da haka, shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai, ya bayyana irin kokarin da hukumar sojin ta ke yi wurin yaki da ta'addanci a kasar nan, musamman ma a jihohi irin su, Zamfara, Katsina, Kaduna, Niger, da kuma wani yanki na babban birnin tarayya Abuja

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel