Yaki da masu satar mutane: An damke yan bindiga 46, an kashe 10 - Sifeto Janar

Yaki da masu satar mutane: An damke yan bindiga 46, an kashe 10 - Sifeto Janar

Mukaddashin sifeto janar na hukumar yan sanda, IG Mohammed Adamu, ya bayyana cewa an damke yan bindiga 46 kuma an hallaka goma tun lokacin da ya kaddamar da atisayen 'Puff Adder' domin yakar masu garkuwa da mutane.

IGP Mohammad Adamu ya kaddamar da atisayen ne ranar 5 ga watan Afrilu, 2019.

Adamu wanda ya laburta hakan a hedkwatan hukumar yan sanda dake birnin tarayya Abuja a wata ganawa da kwamishanonin hukumar yan sanda da mataimakan sifeton yan sandan Najeriya gaba daya.

Ya ce kawo yanzu an kwato makamai 18 wanda ya kunshi bindigar AK47 tara da bindigogin gargajiya tara.

Ya bayyana cewa ganawar zai taimaka wajen duba irin nasarorin da aka samu a atisayen da aka kaddamar domin kawar da masu garkuwa da mutane, fashi da makami, da kuma barandanci.

Ya ce an kaddamar da atisayen 'Puff Adder' ne domin kawar da rashin tsaron da ya addabi jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina da Kogi.

A bangare guda, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyanawa sifeto janar na yan sanda, Muhammad Adamu da duniya cewa yan bindiga da garkuwa da mutane sun kwace wasu sassan jihar daga hannunsa.

Ya laburta hakan ne ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, 2019 inda yake cewa wasu kananan hukumomin jihar dake daura da jihar Zamfara da abin ya shafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel