Rashin kwazo: IGP zai saka wa kwamishinonin 'yan sanda na jihohi takunkumi

Rashin kwazo: IGP zai saka wa kwamishinonin 'yan sanda na jihohi takunkumi

Mukaddashin shugaban rundunar 'yan sanda na kasa, Mohammed Adamu, ya yi barazanar saka wa kwamishinonin 'yan sanda na jihohi takunkumi a kan rashin kwazo da sakaci da aiki a jihohinsu.

Adamu ya bayyana hakan ne yayin gana wa da manyan jami'an 'yan sanda masu mukamin kwamishina zuwa sama, wanda aka yi ranar Alhamis a Abuja.

"Ina mai kira gare ku da ku koma jihohinku domin sabunta salon shugabancinku da zai dace da tsarin aikin dan sanda kamar yadda ya ke a fadin duniya, irin wanda ake bukata domin samun raguwar aiyukan ta'addanci," a cewar sa.

Ya buka ce su bullo da sabbin sare-tsare da hikimomi domin magance aiyukan ta'addanci.

"Dole ku san yadda za ku yi amfani da ikon da ku ke da shi domin kawar da duk wani aikin ta'addanci da kalubalen tsaro.

Rashin kwazo: IGP zai saka wa kwamishinonin 'yan sanda na jihohi takunkumi

IGP Mohammed Adamu
Source: Original

"Zamu iya samun iya samun nasara a kan 'yan ta'adda ne ta hanyar daukan matakan da zasu taimaka wa yakin da muke yi da ta'addanci," a cewar IGP Adamu.

Shugaban na rundunar 'yan sanda ya bayyana cewa za a iya cimma hakan ne ta hanyar hada kai da jama'a tare da dawo da kimar aikin dan sanda.

Legit.ng ta kawo maku labarin cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake gana wa da shugabannin hukumomin tsaro a fadar sa da ke Abuja.

DUBA WANNAN: Kotu ta dakatar da yanke hukunci a kan karar neman a kori Saraki da wasu sanatoci 55

Shugabannin rudunonin sojan sama, kasa da na ruwa da shugaban rundunar 'yan sanda na kasa (IGP) da takwaransa na hukumar tsaro ta farin kaya sun halarci taron domin gabatar da jawabi ga shugaba Buhari a kan yanayin tsaro da kuma kalubalen da suke fuskanta.

Da yake gana wa da manema labarai jim kadan bayan ganawarsu, ta tsawon fiye da sa'a biyu, da shugaba Buhari, shugaban rundunar tsaro ta kasa, Janar Gabriel Olanisakin, ya bayyana cewar shugaban kasa ya basu umarni su nuna rashin tausayi wajen murkushe 'yan bindigar jihar Zamfara da ragowar 'yan ta'adda a sassan kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel