Ka ambaci sunayen sarakunan da ked a hannu a fashi ko ka fuskanci doka – Majalisar sarakunan Zamfara ga ministan tsaro

Ka ambaci sunayen sarakunan da ked a hannu a fashi ko ka fuskanci doka – Majalisar sarakunan Zamfara ga ministan tsaro

- Majalisar sarakunan jihar Zamfara sun mayar da martani ga zargin da ministan tsaro, Mansur Dan Ali yayi a kansu

- Sun karyata cewar wasu sarakuna a Zamfara na da hannu a ayyukan yan bindiga a jihar

- Majalisar ta kalubalance shi da ya ambaci sunayen sarakunan ko kuma su dauki mataki a kansa

Majalisar sarakunan jihar Zamfara sun karyata zargin da ministan tsaro, Mansur Dan Ali yayi a kansu; cewa wasu sarakuna a jihar na da hannu a ayyukan yan bindiga a jihar.

Mai kawo wa Legit.ng rahoto a Zamfara, Lawal Tsalha, ya rahoto cewa an bayyana hakan en a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu, biyo bayan wani taron gaggawa da majalisar sarakunan jihar ta gabatar a ma’aikata kananan hukuma da lamuran sarauta.

Kakakin majalisar, Sarkin Bungudu, Alhaji Muhammad Attahiru, yayi kira ga ministan tsaron da ya kira sunan sarakunan da ke da hannu a fashin kamar yadda yake a zarginsa.

Ka ambaci sunayen sarakunan da ked a hannu a fashi ko ka fuskanci doka – Majalisar sarakunan Zamfara ga ministan tsaro

Ka ambaci sunayen sarakunan da ked a hannu a fashi ko ka fuskanci doka – Majalisar sarakunan Zamfara ga ministan tsaro
Source: UGC

Majalisar tace tana jiran martanin ministan ko kuma za su dauki mataki da ya kamata a kansa.

Sannan majalisar ta yaba da kokarin gwamnatin tarayya wajen daidaita lamarin tsaro a jihar.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisa: Wamakko ya karyata fadin cewa sanatoci 82 na goyon bayan Ahmed Lawan

Majalisar sarakunan ta bukaci sojoji dasu yi taka-tsantsan yayin saka bam a wuraren da ake zargin na yan iska ne kaamar yadda abu ke shafar mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel