Buratai ya yi karin haske akan kashe-kashen jihar Zamfara

Buratai ya yi karin haske akan kashe-kashen jihar Zamfara

- Buratai ya bayyanawa mannema labarai irin kokarin da rundunar soji ta ke yi wurin kawo karshen 'yan ta'addar jihar Katsina

- Ya bayyana cewa tsaro ya fara daga kan mataki na farko har zuwa mataki na karshe, kuma su na bakin kokarin su wurin kawo karshen rikicin a jihar

A wata zantawa da ya yi da manema labarai, shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai, ya bayyana irin kokarin da hukumar sojin ta ke yi wurin yaki da ta'addanci a kasar nan, musamman ma a jihohi irin su, Zamfara, Katsina, Kaduna, Niger, da kuma wani yanki na babban birnin tarayya Abuja

Wata tambaya da wani dan jarida ya yi wa shugaban sojojin Najeriya, inda ya ke tambayarshi kamar haka:

"Game da sha'anin tsaro a jihar Zamfara wasu na ganin kamar sojojin Najeriya sun gaza bisa la'akari da abin da ke faruwa, me za ka ce?"

Shugaban rundunar sojin ya bada amsa kamar:

"To duk wanda ya ce jami'an tsaro sun gaza a kasar nan, bai san abinda ya ke gudana ba, kuma bai san komai game da jami'an tsaro ba.

Buratai ya yi karin haske akan kashe-kashen jihar Zamfara

Buratai ya yi karin haske akan kashe-kashen jihar Zamfara
Source: Twitter

"In ka duba tsaro ya fara daga kan kowanne mutum, wala Allah magidanci, ko saurayi, ko tsoho, da dukkanin jama'an gari tsaro yana kansu. Saboda haka idan aka fara daga tushen abin za'a samu magani kowanne lokaci.

KU KARANTA: An yi karon batta tsakanin 'yan ta'adda da 'yan kungiyar sa kai a Katsina

A karshe shugaban rundunar sojin, ya bayyana irin kokarin da rundunar sojin ta kasa ta ke yi wurin kawo karshen rikicin 'yan ta'adda da ya ke addabar al'ummar kasar nan.

A jihar Zamfara dai an kashe mutane sama da 3,500 a cikin shekaru biyar da suka gabata, sannan an yiwa sama da mutane 9000, raunuka, a bayanin da sakataren gwamnatin jihar Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi ya yi wa manema labarai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel