Hadiza Bala Usman tana so Mata su rika shiga sahun gaba a wurin aiki

Hadiza Bala Usman tana so Mata su rika shiga sahun gaba a wurin aiki

Mun samu labari daga jaridar Premium Times cewa shugaban hukumar tashar ruwan Najeriya, Hadiza Bala Usman, ta koka da cewa jinsin ‘Ya ‘ya mata su ne wadanda su ka fi fuskantar wahala a Duniya.

Shugabar NPA na kasa, Hajiya Hadiza Bala Usman ta bayyana cewa dole a rika damawa da ‘Ya ‘ya Mata wajen ganin cigaban kasa a Duniya. Babbar Manajar ta NPA na Najeriya tayi wannan bayani ne a karshen makon da ya gabata.

Bala Usman ta bayyana wannan ne a lokacin da ta ke jawabi wajen wani babban taro da jami’ar Maritime ta Najeriya ta shirya. Bala Usman din tayi magana ne a kan wani maudu’i da ya shafi harkar mata wajen harkar aikin ruwa.

Babbar Manajar ta tashar ruwan Najeriya ta nemi a rika kafa wata da’ira ta musamman ta ‘ya ‘ya mata a kowace Ma’aikata da su rika kai kukan abin da yake damun su. Hakan zai bada damar shawo kan matsalolin ‘ya ‘ya matan.

KU KARANTA: Asarar Biliyan 90 ta sa za a binciki hukumar wuta a Najeriya

Hadiza Bala Usman tana so Mata su rika shiga sahun gaba a wurin aiki

Hajiya Hadiza Bala Usman ta taba neman takarar kujerar Majalisa
Source: UGC

Bala Usman a jawabin na ta, ta ba gwamnati shawarar ta rika maida hankali wajen ilmantar da matan da ke da sha’awar ilmin harkar ruwa. Usman ta na so a ba Mata kwarin gwiwa kwarewa a harkar kimiyya, da Ingilishi da ilmin lissafi.

A jawabin na shugabar NBA ta bada shawarar hanyoyin da ya kamata a bi wajen samun daidaito tsakanin Mata da kuma Maza a wuraren aiki. A cewar ta, kusan a kowace ma’aikata ko bangare, ana nunawa Mata banbanci a kan Maza.

Hajiya Hadiza Usman, ta taba rike mukamin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Kaduna, kafin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta nada ta a matsayin shugabar hukumar NBA na kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel