Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta ceto Leah Sharibu daga hannun Boko Haram

Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta ceto Leah Sharibu daga hannun Boko Haram

- Majalisar dattawa ta bukacin gwamnatin tarayya da ta ceto Leah Sharib daga hannun Boko Haram

- Sanata Shehu Sani ya kuma bukaci sakin sauran yan matan Chibok da ke tsare a hannun Boko

- Sani ya janyo hankalin gwamnatin tarayya akan ci gaba da rike Leah Sharibu, inda ya nemi bangaren dokoki su sanya baki domin dawo da ita gida

Majalisar dattawa ta bukacin gwamnatin tarayya da ta nemi sakin yar matar makarantar Dapchi daya da ta saura, Leah Sharibu, daga hannun Boko Haram.

Rokon ya biyo bayan wani umurni daga Sanata Shehu Sani a lokacin zaman majalisa a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu.

Ya janyo hankalin gwamnatin tarayya akan ci gaba da rike Leah Sharibu, inda ya nemi bangaren dokoki su sanya baki domin dawo da ita gida.

Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta ceto Leah Sharibu daga hannun Boko Haram

Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta ceto Leah Sharibu daga hannun Boko Haram
Source: Depositphotos

Sanata Sani ya kuma bukaci sakin sauran yan matan Chibok da ke tsare a hannun Boko.

KU KARANTA KUMA: Zabe: An maka Yakubu Dogara a gaban kotu

An sace Leah Sharibu tare da sauran yan makaranta 111 a ranar 19 ga watan Fabrairun 2018, daga makarantarta, makarantar sakandare na yan mata a Dapchi, jihar Yobe.

Gwamnatin tarayya ta tattauna wajen sakin sauran yan matan amma ba a saki Leah Sharibu ba wacce ta ki barin addininta na Kirista a matsayin fansar sakinta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel