Buhari ya gaggauta kubutar da Leah Sharibu daga hannun BH - Majalisar dattijai

Buhari ya gaggauta kubutar da Leah Sharibu daga hannun BH - Majalisar dattijai

- Majalisar dattijai ta bukaci gwamnati da ta bi dukkanin matakan da suka dace don ganin an kubutar da Leah Sharibu daga hannun mayakan Boko Haram

- Wannan rokon ya biyo bayan wata bukata ta musamman da Sanata Shehu Sani ya gabatar a zaman majalisar na ranar Alhamis

- Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa mayakan Boko Haram sun sace Leah Sharibu tare da sauran 'yan makarantarsu guda 111 a ranar 19 ga watan Fabreru, 2018

Majalisar dattijai ta bukaci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da a bi dukkanin matakan da suka dace don ganin an kubutar da dalibar makarantar Dapchi ta karshe, Leah Sharibu daga hannun mayakan Boko Haram.

Wannan rokon ya biyo bayan wata bukata ta musamman da Sanata Shehu Sani ya gabatar a zaman majalisar na ranar Alhamis.

Ya jawo hakalin gwamnatin tarayyar akan ci gaba da tsare Leah Sharibu da mayakan Boko Haram ke yi, yana mai bukatar majalisar dattijan da ta sa baki don ganin an kubutar da ita tare da sada ta da iyayenta.

KARANTA WANNAN: Matsalar tsaro a Borno: Shettima ya gana Dan-Ali, Buratai da Bichi a Abuja

Buhari ya gaggauta kubutar da Leah Sharibu daga hannun BH - Majalisar dattijai

Buhari ya gaggauta kubutar da Leah Sharibu daga hannun BH - Majalisar dattijai
Source: Depositphotos

Sanata Sani ya kuma bukaci da kubutar da dukkanin 'yan matan Dapchi da ke hannun Boko Haram.

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa mayakan Boko Haram sun sace Leah Sharibu tare da sauran 'yan makarantarsu guda 111 a ranar 19 ga watan Fabreru, 2018, a makarantar sakandiren kimiya da fasaha ta gwamnati da ke garin Dapchi, jihar Yobe.

Gwamnatin tarayya ta yi yarjejeniya da mayakan Boko Haram inda har aka saki sauran 'yan matan, amma duk wani yunkuri na kubutar da Leah Sharibu ya ci tura, sakamakon kin amincewarta na barin addininta na Kirista.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel