Kotu ta dakatar da yanke hukunci a kan karar neman a kori Saraki da wasu sanatoci 55

Kotu ta dakatar da yanke hukunci a kan karar neman a kori Saraki da wasu sanatoci 55

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da yanke hukunci a kan karar da wata kungiya, 'Legal Defence and Assistance Project (LEDAP)', ta shigar a kan neman a kori shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da wasu sanatoci 55.

LEDAP ta shigar da karar Saraki da ragowar sanatoci 55 bisa hujjar cewar su ba mambobin majalisar dattijai ba ne saboda sun canja sheka zuwa wasu jam'iyyu kafin karewar wa'adinsu.

Kungiyar, a takardar karar da suka shigar, sun nemi kotu ta fassara sashen 68(1)(g) na kundin tsarin mulki na shekarar 1999.

Sashen na da alaka da batun matsayin mamba a majalisar tarayya bayan ya fita daga cikin jam'iyyar da ya ci zabe kafin karewar zangonsa.

Kungiyar na neman kotun ta bayyana mambobin a matsayin haramtattu, sannan su mayar wa da gwamnatin tarayya dukkan alabashi da alawus-alawus da suka karba bayan sun canja sheka.

A cikin takardar karar, LEDAP ta nemi kotu ta tilasta shugabannin majalisa su bayyana duk wanin mamba da ya canja sheka a matsayin haramtacce.

Kotu ta dakatar da yanke hukunci a kan karar neman a kori Saraki da wasu sanatoci 55

Majalisar dattijai
Source: Depositphotos

Kotun, bayan ta gamsu da hujjojin masu kara tare da aika sammaci ga duk wadanda aka shigar kara amma suka ki amsa kiranta, ta bawa masu kara damar gabatar da hujjojinsu, wanda bayan hakan ne ta tsayar da ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu domin yanke hukunci.

Da aka kira karar a yau, Alhamis, domin yanke hukunci, lauyan da ke kare Saraki da sauran sanatocin, Mista Mahmud Magaji, ya roki kotun da ta jinkirta yanke hukunci omin bawa wadanda ake kara damar kare kansu da kuma samun hukunci na adalci.

DUBA WANNAN: Ambaliyar ruwan sama ta rushe gidaje 48, ta raba mutane 285 da gidajensu a jihar Filato

Sai dai, Lauyan kungiyar LEDAP, Mista Ede Uko, ya soki bukatar takwaransa da ke kare Saraki da sauran Sanatocin, ya na mai bayyana cewar hakan wani yunkuri ne kawai na kawo tsaiko ga yanke hukunci a kan shari'ar.

Da yake raddi a kan mahawarar lauyoyin, alkalin kotun, Jastis Okon Abang, ya ce duk da ya amince da hujjar lauyan masu kara, yanke hukunci a wannan lokaci zai kasance tamkar aikata kuskure ne a wurin kotun, saboda rashin jin ta bakin wadanda ake kara.

Daga bisani ya daga sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Afrilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel