An gurfanar da wasu mata uku da suka tara wa wani dan sandan gajiya

An gurfanar da wasu mata uku da suka tara wa wani dan sandan gajiya

A yau Alhamis ne aka gurfanar da wasu mata 'yan kasuwa uku da suka yiwa wani jami'in dan sanda duka yayin da ya ke gudanar da aikinsa a gaban kotun Majistare da ke Ikeja a Legas.

Matan Fatimoh mai shekaru 47, Mutiat mai shekaru 32 da Dupe mai shekaru 41 duk mazauna mushin suna fuskantar tuhumar laifin tayar da zaune tsaye, kin amincewa a kama su da hadin baki tare da yiwa wani rauni.

A cewar mai shigar da karar, Sufeta Aondohemba Koti, wadanda akayi karar sun aikata laifin ne a ranar 23 ga watan Maris a unguwar Mushin a jihar Legas.

Ya ce wadanda a kayi karar sun yiwa mataimakin sufritanda Abayomi Adejumo da sufeta Oluseun Adelaja duka yayin da suke kokarin yin sulhu.

DUBA WANNAN: Zargin Madigo: Yadda Hadiza Gabon ta titsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari

Wasu mata uku da suka yiwa dan sanda duka sun gurfana gaban kuliya

Wasu mata uku da suka yiwa dan sanda duka sun gurfana gaban kuliya
Source: Twitter

"An yiwa 'yan sandan duka ne yayin da suke kokarin yin sulhu tsakanin wadanda a kayi kara da wasu ma'aikatan hukumar lantarki.

"Koti ya ce wadanda akayi karar sun tayar da hankalin al'umma ne lokacin da suka kwace ladar Hukumar Rabar da Wutan Lantarki ta Eko yayin da suke kokarin yanke musu wuta.

"Wadanda akayi karar kuma sun hana James, Adewale da Gideon gudanar da aikinsu a matsayin jami'an hukumar wutan lantarki.

"Bayan jami'an wutan lantarkin sun yanke wutan wadanda akayi kara, sun kwace ladar sun zauna a kanta sunce ba za su bayar da ita ba har sai an mayar musu da wutarsu.

"Jami'an hukumar lantarkin sun kira 'yan sandan ne a lokacin da suka lura cewa lamarin ya fi karfinsu sai dai ko da yan sandan suka iso, ba su bayar da ladar ba sai suka yiwa 'yan sandan duka.

"Wadanda akayi karar sunki amince a kama su amma daga bisani an tilasta su zuwa caji ofis," inji mai shigar da karar.

Sai dai wadanda akayi karar sun musanta zargin da ake musu.

Abinda ake zarginsu da aikatawa ya sabawa sashi na 168, 117, 174 da 411 na dokar masu aikata laifi na jihar Legas na 2015.

Alkaliyar kotun, Mrs M.O Tanimola ta bayar da belin su a kan kudi N60,000 kowanensu tare da gabatar da mutum daya da zai karbi belin kowannen su.

Kotun ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Afrilun 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel