Matsalar tsaro a Borno: Shettima ya gana Dan-Ali, Buratai da Bichi a Abuja

Matsalar tsaro a Borno: Shettima ya gana Dan-Ali, Buratai da Bichi a Abuja

- Gwamna Kashim Shettima na jihyar Borno ya gana da Mansur Dan-Ali; Laftanal Janar Tukur Buratai, da kuma Yusuf Bichi, kan matsalolin tsaro da jihar

- Ganawar dai ta fi mayar da hankali kan kwashe al'ummar garin Jakana da ke Konduga zuwa ga wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Maiduguri

- Gwamna Shettima ya ce ganawar tsakanin jihar Borno da shuwagabannin tsaron ta haifar da d'a mai ido

Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno, tare da wasu mambobin majalisar dokokin jihar, a ranar Laraba, sun kai ziyara tare da ganawar sirri da ministan tsaro, Mansur Dan-Ali; hafsan rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, da kuma babban daraktan hukumar tsaro ta DSS, Yusuf Bichi, dangane da matsalolin tsaro da jihar Borno ke fuskanta.

Ganawar dai ta fi mayar da hankali kan matsalolin tsaro da suka hada da kwashe al'ummar garin Jakana da ke cikin karamar hukumar Konduga zuwa ga wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Maiduguri, inda jami'an soji a jihar Borno suka ce sun yi hakan ne domin ci gaba da yaki da Boko Haram.

Shettima ya samu rakiyar shugaban kwamitin majalisar dokokin jihar kan tsaro, Abubakar Kyari da Betara Aliyu; shugaban kwamitin dokoki da kasuwanci na majalisar dattijai, Baba Garbai, da kuma wasu zababbun 'yan majalisun tarayya guda biyu.

KARANTA WANNAN: Saboda harin'yan ta'adda: Al'ummar Zamfara za su samu tallafin N10bn na jin-kai

Matsalar tsaro a Borno: Shettima ya gana Dan-Ali, Buratai da Bichi a Abuja

Matsalar tsaro a Borno: Shettima ya gana Dan-Ali, Buratai da Bichi a Abuja
Source: Facebook

Gwamnan tare da tawagarsa sun fara ganawa da daraktan hukumar tsaro ta DSS a shelkwatar hukumar da misalin karfe 1:30 na rana, kafin haduwa da ministan tsaro a wani gida da misalin karfe 4 na yamma, inda daga bisani tawagar ta dira shelkwatar rundunar soji da misalin karfe 5 tare da ganawa da hafsan rundunar sojin, har tsawon sama da awa daya.

Gaba daya ganawar an yi su ne a sirrance a Abuja.

Da ya ke yiwa manema labarai bita, gwamna Shettima ya ce ganawar anyita ne domin tattauna batutuwan da suka shafi kwashe al'ummar Jakana, Auno da Mainok da ke cikin karamar hukumar Konduga a jihar Borno zuwa sansanin 'yan gudun hijira.

Ya ce ganawar tsakanin jihar Borno da shuwagabannin tsaron ta haifar da d'a mai ido.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel