Yan asalin Abuja sun yi zanga-zanga a majalisar dokokin kasa

Yan asalin Abuja sun yi zanga-zanga a majalisar dokokin kasa

Wata kungiya na yan asalin babban birnin tarayyar kasar sun gudanar da wata zanga-zanga a majalisar dokokin kasar da ke Abuja.

Masu zanga-zangar a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu sun yi Allah wadai da kisan wani Hamza Haruna da ake zargin jami’an tsaro da aikatawa a birnin tarayyar kasar.

A wata wasika zuwa ga Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, kungiyar tayi zargin cewa anyi wa yan asalin Abuja fashin kayansu.

Sun kuma yi ikirarin cewa an sayar masu da filayensu sannan kuma sunce masu mamayar na lalata masu albarkatun gonakinsu.

Yan asalin Abuja sun yi zanga-zanga a majalisar dokokin kasa

Yan asalin Abuja sun yi zanga-zanga a majalisar dokokin kasa
Source: Facebook

Wasikar, na dauke da kwanan wata 11 ga watan Afrilu, 2019, dauke da sa hannun jagoran kungiyaar, Kamal Shuaib.

KU KARANTA KUMA: Rushewar gini: An ruguza gajiyayyun gine-gine 30 a Lagas

A wani lamari na daban mun ji cewa Babban hadimin shugaban kasa akan harkar samar da ayyuka ga matasa, Afolabi Imoukhuede ya tabbatar ma matasan dake cin gajiyar tsarin daukan aiki na gwamnatin tarayya na N-Power cewa zasu sau albashinsu na watan Maris cikin satin nan.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Afolabi ya bada wannan tabbaci ne a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, yayin da yake musanta zargin da wasu ke yi na danganta nukusanin biyan albashin ga dabarar dakatar da biyan N-Power gaba daya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel