Tsaro: 'Yan sanda sun cafke 'yan fashi da makami biyu a Zaria

Tsaro: 'Yan sanda sun cafke 'yan fashi da makami biyu a Zaria

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta ce jami'anta sun dakile wata yunkurin aikata fashi da makami a garin Dumbin Rauga a wajen garin Zaria inda kuma suka kama biyu daga cikin 'yan fashin.

Wata kwakwarar majiya daga rundunar 'yan sandan da ta nemi a boye sunanta ta shaidawa kamfanin dillancin labarai, NAN a Zaria cewa tawagar 'yan sandan masu sintiri na Saye Division ne suka kama 'yan fashin misalin karfe 1.20 na dare kusa da Asiibitin Kutare bayan sunyi musayar wuta.

Majiyar ta ce wadanda aka kama sun hada da Abdulhamid Tanimu mazaunin Dumbin Rauga da Mohammed Murtala daga Karu Abuja yayin da sauran 'yan fashin uku sun tsere.

'Yan sanda sun katsewa wasu 'yan fashi da makami hanzari a Zaria

'Yan sanda sun katsewa wasu 'yan fashi da makami hanzari a Zaria
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Zargin Madigo: Yadda Hadiza Gabon ta titsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari

"Yan sandan sunyi gamo da mutane biyar a cikin mota kirar Honda Civic mai launin kore tare da guda cikinsu sanye da kayan sojoji.

"Daga ganin 'yan sandan sai 'yan fashin suka canja hanya suka nufi hanyar Kanfanin Madaci domin su tsere sai dai 'yan sandan sunyi zargin bata gari ne kuma suka bi su.

"A yayin da suke kokarin gudu, daya daga cikin 'yan fashin ya yi yunkurin harbin dan sanda da bindiga kirar AK 47 amma bai yi sa'a ba kuma daga bisani aka kama su bayan musayar wuta."

Abubuwan da aka kwato hannunsu sun hada da bindiga kirar AK 47, alburussai masu yawa, adduna uku da kuma layyu da guru masu yawa.

A lokacin da ya ke amsa tambayoyin 'yan sanda, daya daga cikin wadanda aka kama ya amsa cewa sune suke fitinar al'umma a garin Dumbin Rauga musamman hanyar Kaduna zuwa Zaria.

A yayin da ya ke tabbatar da lamarin, Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo ya ce an fara gudanar da bincike a kan lamarin kuma ya yi kira ga al'umma su cigaba da bawa 'yan sanda hadin kai da goyon baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel