Rashin tausayi: Matsafa sun halaka dattijuwa mai shekaru 50

Rashin tausayi: Matsafa sun halaka dattijuwa mai shekaru 50

Al'ummar garin Arigidi Akoko da ke karamar hukumar Aloko North West na jihar Ondo sun shiga dimuwa da juyayi bayan wasu da ake zargi matsafa ne sun kashe wata dattijuwa mai shekaru 50, 'Iya Dunsi'.

Channels TV ta ruwaito a ranar Alhamis cewa dattijuwar tana sayar da man ja ne a garin kafin a kashe ta.

An tsinci gawar ta kimanin mita 100 daga gidanta da ka garin na Arigidi Akoko.

DUBA WANNAN: An gwabza tsakanin leburori hausawa da matasa a Benin, mutum biyu sun jikkata

Rashin tausayi: Matsafa sun halaka dattijuwa mai shekaru 50

Rashin tausayi: Matsafa sun halaka dattijuwa mai shekaru 50
Source: Depositphotos

A yayin da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin, Kwandan 'yan sanda na Ikare-Akoko, Razak Rauf ya ce ba zai bari miyagun mutane su rika cin karen su babu babbaka ba a yankinsa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Femi Joseph shima ya tabbatarwa majiyar Legit.ng kisar dattijuwan.

Ya ce matar tana hanyarta na dawowa daga arewa ne inda ta tafi sayo kayayakin da za ta sayar.

Joseph ya kara da cewa ta dawo garin da sanyin safiyar Laraba kafin daga bisani miyagun suka kashe ta.

Ya ce rundunar yan sanda ta fara bincike domin gano miyagun da suka aikata wannan mummunan aikin domin su fuskanci shari'a.

A shekarar 2018, an samu irin wannan kashe-kashen na matsafa har guda uku a Ikare-Akoko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel