Zabe: Abokin hamayyar Yakubu Dogara ya maka shi a kotu

Zabe: Abokin hamayyar Yakubu Dogara ya maka shi a kotu

Rahotanni sun kawo cewa an shigar da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara kara a gaban kotun sauraron kararrakin zabe.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa ana kalubalantar nasarar Dogara a zaben yan majalisa da ya gudana a jihar daga cikin kararraki 27 da aka shigar kotun zaben.

Wannan dai shine karo na hudu da kakakin majalisar ke komawa majalisar dokokin kasar.

Dogara dai ya samu nasarar kayar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC Dalhatu Abubakar da tazarar kuri’u masu yawa a kujerar dan majalisar tarayya da ke wakiltar mazabar Tafawa Balewa, Bogoro da kuma Dass.

Zabe: An maka Yakubu Dogara a gaban kotu

Zabe: An maka Yakubu Dogara a gaban kotu
Source: Twitter

Sakataren kotun amsar kararrakin zabe a jihar Bauchi, Alhaji Bello G. Abdullahi, ya shaida cewar kawo lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida kesa-kesai guda 27 ne aka shigar a gabansu ana kalubantar zabe a kujeru daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Rushewar gini: An ruguza gajiyayyun gine-gine 30 a Lagas

Majiyarmu ta rahoto cewa daga cikin kwafin kesa-kesai 27 da kotun ta amsa kana da manna su a gaban kotun domin kowa ya gansu, akwai karar da Hon. Dalhatu Abubakar Abdullahi na jam’iyyar APC ya shigar wanda ke nuna rashin gamsuwarsa da nasarar da Yakubu Dogara ya samu a kujerar Majalisar tarayya da ke wakiltar mazabar Dass/ Tafawa Balewa/Bogoro. Shi dai Dalhatu shine suka yi takara da Dogara, inda Dogaran ya kayar da shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel