Lai Muhammed ya caccaki Atiku Abubakar

Lai Muhammed ya caccaki Atiku Abubakar

- Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya yi kaca-kaca da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar

- Ministan ya ce idan Atiku bai bi a hankali ba zai iya jefa kanshi cikin matsala babba, wacce za ta sa dole doka ta hau kanshi

A yau Alhamis dinnan ne 11 ga watan Afrilu, gwamnatin tarayya ta gargadi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, akan kada ya yi wani abu da zai iya saka shi cikin damuwa, a kokarin da yake na kwace kujerar shugaban kasa, bayan 'yan Najeriya sun ki zabar shi a zaben da aka gudanar wannan shekarar.

Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed shine ya yi gargadin yau a Abuja, lokacin da suke ganawa da manema labarai shi da mai taimakawa shugaban kasa na musamman, Malam Garba Shehu.

Lai Muhammed ya caccaki Atiku Abubakar

Lai Muhammed ya caccaki Atiku Abubakar
Source: Depositphotos

Ministan ya ce laifi ne babba irin hanyoyin da Atiku ya ke bi, wadanda sun sabawa dokar kasa wajen ganin ya karbi mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari, bayan kuma ya riga ya shigar da kara kotu, kuma yanzu haka ana sauraron karar tashi.

Ministan ya kara da cewa Najeriya kasa ce wacce ta ke cike da dokoki, saboda haka duk wata hanya da mutum ya bi wacce ta sabawa dokar kasa, zai iya fuskantar fushin hukuma, kuma dole za a dauki mataki kwakkwara akan shi.

KU KARANTA: Dangote ya bayyanawa matasa hanyar da za su zama kamar shi

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar dai ya sha kasa a gurin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya fito a babbar jam'iyya mai mulki ta APC, a zaben da aka gudanar ranar 9 ga watan Fabrairun wannan shekarar.

Sai dai kuma Atiku Abubakar ya nuna rashin amincewarshi ga sakamakon zaben, inda ya nufi kotu ya kai karar hukumar zabe ta kasa da kuma jam'iyyar APC, akan cewar shine ya lashe zaben aka murde aka ba wa shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel