An samu rahoton barkewar cutar sankarau har guda 4 a Bauchi

An samu rahoton barkewar cutar sankarau har guda 4 a Bauchi

-Cutar sankarau ta barke a jihar Bauchi, an samu labarin cutar har guda hudu a fadin jihar ta Bauchi ranar Alhamis.

-Kwana a cikin daki a cinkushe da kuma rashin yalwar isaka dake iya keyawa cikin dakin shine abinda ke haifar da wannan cutar.

Gwamnatin jihar Bauchi ta samu labarin wuraren da ake tsammanin cewa akwai cutar sankarau jihar.

Mallam Adamu Gamawa, wanda shine shugaban kula da lafiya na matakin farko a jihar ya shaidawa manema labarai akan barkewar cutar a Bauchi ranar Alhamis.

Asibiti

Asibiti
Source: Twitter

KARANTA WANNAN:Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock

Gamawa yace, daya daga cikin matsalolin na tabbatar da ita inda yace itace kwayar cuta a yaren kimiyya wanda ake kira ‘Streptococcus Pneumonia’ inda ya bayyana cewa ita din bata aukuwa a matsayin annoba.

Ya kara da cewa, matsalar kuwa guda nan ana gwaji akai domin a tantance ko sankarau ce ko kuma wata cutar daban, wanda hakan zai iya samuwa ne bayan an kamala binciken.

Gamawa har ila yau, ya shawarci jama’a da su guji kwana cikin cinkoso da kuma dakunan da basu da yelwar shiga da fitar isa hakan shike haifar da yaduwar wannan cuta.

Ya kuma roki mutane da suyi gaggawar kai rahoton duk wani sauyi da suka gani zuwa ga asibiti mafi kusa da su ko kuma ma’aikatar lafiya mafi kusa.

A wani labarin kuwa, hukumar INEC ta lashi takobin cewa lallai ba zata baiwa gwamanan jihar Imo, Rochas Okorocha takardar shahadar nasara a zaben majalisar dattawa ba.

Hukumar ta INEC tace sam Okorocha ba zai samu takardar shahadar ba daga wurinta saboda wasu hujjoji da take dasu akan gwamnan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel