Yanzu Yanzu: Sojojin Sudan sun hambarar da Omar al-Bashir bayan shekaru 30

Yanzu Yanzu: Sojojin Sudan sun hambarar da Omar al-Bashir bayan shekaru 30

Rundunar sojojin kasar Sudan sun tsige Shugaban kasar Omar al-Bashir daga kan mulki, biyo bayan watanni da aka kwashe ana zanga-zanga a wajen ma’aikatar tsaro a tsakiyar Khartoum.

A wani jawabi, mistan tsaron kasar Sudan kuma babban janar na sojoji Ahmed Awad Ibn Auf yace an kama Bashir, wanda ya shefe shekaru 30 yana mulki “an killace shi a wani wuri na musamman”. Sojoji za su tafiyar da mulkin kasar na tsawon shekaru biyu, inda za a gudanar da zabe, inji ministan.

Harila yau, ministan tsaron kasar ya bayyana cewa za a lura da hakkin dan adam kuma ya bukaci 'yan kasar da su yi hakuri da matakan da sojoji za su dauka a kasar.

Rundunar Sojoji sun hambarar Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir

Rundunar Sojoji sun hambarar Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir
Source: UGC

Dakarun sojin na Sudan sun kewaye gidan Talabijin na kasar tare da shiga cikinsa. Haka zalika an hana tashin jiragen sama a Khartoum inda ake bayar da izinin sauka kawai.

An tattaro inda ministan tsaron na cewa: "Za a kama Omar al-Bashir a kai shi kebaben wuri da za a kula dashi. Za a sa dokar ta baci a kasar na tsawon wata uku.

"Sojoji za su kula da kasar a lokacin wa'adin da aka kebe na shirye-shiryen mika mulki. Za a kafa wani kwamiti na sojoji da za su kula da shirye-shiryen mika mulki.

"Za a soke amfani da kundin tsarin mulki na 2005."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel