Rushewar gini: An ruguza gajiyayyun gine-gine 30 a Lagas

Rushewar gini: An ruguza gajiyayyun gine-gine 30 a Lagas

A kokarin guje wa sake aukuwar rushewar gine-gine a jihar Lagas, hukumar kula da gine-gine na jihar Lagas (LASBCA), tace ta rusa gine-gine 30 cikin 80 wadanda aka yi ma alamar rusawa a birnin Lagas.

Mista Olalekan Shodehinde, Babban Manajan LASBCA, ya fada ma Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a ranar Laraba, 11 ga watan Afrilu a Legas cewa za a gudanar da rushe-rushen ne a kan tsari saboda wasu gin-ginen sun kasance da kararaki a kotu.

Yace gine-ginen da aka rusa sun hada da na unguwar Elegbata, Apongbon; unguwar Tokunbo, unguwar Inabiri, unguwar Egatin, Ojo Giwa, unguwar John, da sauran su.

Shodehinde ya fada cewa an sanya alama akan gine gine 80 don rusawa bisa zubewa da wata ginin bene tayi a ranar 13 ga watan Maris a yankin Ita Faji dake Lagos Island wanda yayi sanadiyyan mutuwar mutane 20.

Rushewar gini: An ruguza gajiyayyun gine-gine 30 a Lagas

Rushewar gini: An ruguza gajiyayyun gine-gine 30 a Lagas
Source: UGC

Shugaban LASBCA ya bayyana cewa an kafa kwamiti don gudanar da bincike kan zubewar gini a Ita Faji.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sojojin Sudan sun hambarar da Omar al-Bashir bayan shekaru 30

Yace hukumar tana kan gudanar da aiki don kammala tsarin da zai kawo hadin kai tsakanin kwararrun hukumomi da hukumomi masu zaman kansu a yaki da ruguzowar gine-gine.

Shodehinde ya roki al’umma da dukkan masu ruwa da tsaki da su taimaki gwamnati wajen ganin ta cimma burinta na tsare Lagas tare da bada rahotanni akan gine-gine marasa tsari a wurarensu don daukar mataki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel