Lawan zai samu kuri’u 2/3 don zama Shugaban majalisar dattawa – Kakakin majalisar dattawa

Lawan zai samu kuri’u 2/3 don zama Shugaban majalisar dattawa – Kakakin majalisar dattawa

- Akwai tabbacin cewa Sanata Ahmad Lawan zai zamo Shugaban majalisar dattawa na gaba

- Daya daga cikin takwarorinsa, Sanata Abdullahi Sabi, ya bayyana cewa Lawan zai samu kaso biyu cikin uku na kuri’ u don zama zakara

- Sabi ya bayyana cewa hakan mai yiwuwa ne ta hanyar taimako da goyon bayan sanatocin jam’ iyyar All Progressives Congress (APC) a majalisar

Kakakin majalisar dattawa, Sanata Abdullahi Sabi ya nuna tabbacin cewa takwaransa, Ahmad Lawan, zai lashe kuri’un kaso biyu cikin uku don zama Shugaban majalisar dattawan.

Sabi, wanda ya bayar da tabbacin yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu a Abuja, yace da amincewar jam’ iyyar All Progressives Congress’ (APC) da kuma tabbacin da yake samu daga zababbun sanatoci a fadin jam’iyyar, Lawan zai yi nasarar lashe kujerar, kamfanin dillanin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito.

Sanata Sabi (APC-Niger), wanda ya sakie lashe zabe a majalisar dattawa ta 9, yace tuni an fara tattaunawa don marawa Lawan baya wajen ganin ya zama Shugaban majalisar dattawan.

Lawan zai samu kuri’u 2/3 do zama Shugaban majalisar dattawa – Kakakin majalisar dattawa

Lawan zai samu kuri’u 2/3 do zama Shugaban majalisar dattawa – Kakakin majalisar dattawa
Source: Twitter

Ya yi watsi da tsoron cewa shugabancin Lawan zai kawo matsala, inda ya kara da cewa zai janyo dukkanin yan majalisar a jiki domin tafiya tare.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock

Ya ce yayinda yan majalisa ke da yancin yanke hukunci akan abunda ya shafi yankunansu, hukuninsu zai yi adalci ga Lawan.

Ya ce lawan na da tarin kwarewar da zai riki wannan mukamin kasancewar yaa a majalisar dokoki tun 1999.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel