An daga karar tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa

An daga karar tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa

- An daga karar tsohon shugaban jam'iyyar PDP da ta danshi, har zuwa ranar 5 ga watan Yuni

- An daga karar ne bisa damar da kotu ta bawa wanda ake zargin domin fita kasar waje neman magani

Alkalin babbar kotun tarayya dake Abuja, A.R. Mohammed ya bayyana daga sauraron shari'ar tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Halliru Bello da danshi, Bello Abba Mohammed, zuwa ranar 5 ga watan Yuni 2019, inda za a cigaba da sauraron karar.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa ita ce kama tsohon shugaban jam'iyyar PDP da dan nashi da laifin kabar kudi kimanin naira miliyan 300, daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara akan har tsaro Col. Sambo Dasuki (Rtd). Ana tuhumar su da aikata laifuka guda hudu duka wadanda suke da alaka da cin hanci da rashawa, da kuma yin amfani da kudi ta hanyar da bata dace ba.

An daga karar tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa

An daga karar tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa
Source: Twitter

A jiya Laraba ne 10 ga watan Afrilu 2019, lokacin da ya kamata a cigaba da sauraron kara, sai daya daga cikin 'yan kwamitin shigar da karar O.A. Atolagbe, ya bayyana cewa kwamitin ta gama shiryawa da shaidunta, sai ya samu kiran waya da ake fada masa cewa daya daga cikin lauyoyin mai suna Solomon Umeh, SAN, ba zai samu damar zuwa kotun ba.

"Na samu labarin cewa, ya na kotun daukaka kara da ke garin Jos, kuma ba zai samu damar zuwa nan ba," in ji shi.

KU KARANTA: An yi karon batta tsakanin 'yan ta'adda da 'yan kungiyar sa kai a Katsina

Bayan haka kuma, Barth Ogar, daya daga cikin masu kare wadanda ake zargin, ya bayyana cewa ya fita kasar waje neman magani, wanda aka yi dashi cewar zai dawo daga watan Afrilu zuwa watan Mayu. Hakan ya tilasta kwamitin shigar da karar neman kotu ta daga karar, akan yarjejeniyar wanda ake zargin zai bayyana a gaban kotu ranar da za a cigaba da sauraron karar.

A karshe kotun ta bukaci Bello ya rubuta takarda dake nuna cewar zai dawo kotu ranar da za a cigaba da sauraron kara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel