Majalisa za ta tursasa shugaba Buhari ya sanya hannu akan wasu dokoki

Majalisa za ta tursasa shugaba Buhari ya sanya hannu akan wasu dokoki

- Majalisar tarayya ta ce za ta kara maidawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasu dokoki guda biyu da ta bukaci ya sanya hannu yaki

- Majalisar ta ce akwai wasu dokokin guda 15 yanzu haka wanda shugaba Buhari ya ki ya sanya hannu

A jiya Laraba ne majalisar dattijai ta yanke shawarar sake gabatarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari wasu kuduri guda biyu da majalisar ta aika masa wanda yaki saka hannu a kai.

Har ila yau, majalisar ta amince da da sake aikawa shugaban kasar wasu kudurori guda 15 da suma yaki ya sanya hannu a kai.

Kuduri guda biyun da za a aikawa shugaban kasar sun hada "Kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, sannan kuma da kudurin kawo cigaba a harkar gine-gine da masana'antu.

Majalisa za ta tursasa shugaba Buhari ya sanya hannu akan wasu dokoki

Majalisa za ta tursasa shugaba Buhari ya sanya hannu akan wasu dokoki
Source: Twitter

Canjin da za a kawo na gyaran kundun tsarin mulkin, zai canja yadda shugaban kasa ko gwamna zai gabatar da doka a gaban majalisar tarayya ko majalisar jiha.

Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya ki yarda ya sanya hannu a kudurin, saboda ya ce bai fahimci abubuwan da kudurin ya tanadar wanda zai kawo cigaban kasa ba.

A bangaren dokar kudurin gine-gine da masana'antu kuwa, kudurin zai bawa kamfaninnika damar fadada kasuwancin su a fadin kasar nan.

KU KARANTA: An yi karon batta tsakanin 'yan ta'adda da 'yan kungiyar sa kai a Katsina

Bayanai sun nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki sanya hannu akan dokar ne, inda ya bayyana cewa zai yi shawara da ministocinsa kafin ya saka hannu akan dokar.

Rahotanni sun nuna cewa tun lokacin da aka gabatar da majalisar dokoki ta takwas, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi kudurori guda 36 daga majalisar tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel