Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu yayi ganawar sirri da shugabannin tsaro.

An fara ganawar a ofishin Shugaban kasa da ke fadar Shugaban kasa da misalin karfe 11am.

Tattaunawar zai ta’allaka ne akan lamarin da tsaro ke ciki a kasar.

Musamman za a tattauana kan hauhawan hare-haren yan bindiga a jihohin arewa maso yamma, kashe-kashen Kaduna da kuma sace-sacen mutane a wasu yankunan kasar.

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock

Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da shugabannin tsaro a Aso Rock
Source: Twitter

Kan ayyukan yan bindiga a jihar Zamfara, baya ga tura tawaga na musamman da kayayyaki gwamnatin tarayya, a ranar Lahadi ta alakanta fashin da hake-haken ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar.

Sannan tayi umurnin dakatar da ayyukan hake-haken ma’adinai a jihar Zamfara da kewayenta sannan tayi kira ga yan kasashen waje dasu dakatar da ayyukan hake-hake a jihar.

KU KARANTA KUMA: Batan N38bn: Yan majalisar wakilai sun sanya manyan jami’an PenCom a kwana na tsawon sama da sa’o’i 3

A wani jawabi a ranar Talatam shugaba Buhari yayi Allah wadai da rikicin kwanan nan a jihar Kaduna, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 20 a garin Adara.

Ganawarsa da shugabannin tsaro na kan gudana a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel