Boko Haram: Rundunar yan sanda ta ba mutaneen Yobe tabbacin samun kariya

Boko Haram: Rundunar yan sanda ta ba mutaneen Yobe tabbacin samun kariya

- Hukumar yan sandan jihar Yobe tayi kira ga al’umman jihar da su kwantar da hankulansu sannan su ci gaba da harkokin gabansu

- Hakan ya biyo bayan yunkurin kaddamar da hari da yan ta'addan Boko Haram suka yi yunkurin kaiwa wanda sojoji suka yi nasarar dakilewa

- Rundunar yan sandan ta jadadda cewa hukumomin tsaro na nan suna aiki domin ba al'umman yankin kariya

Rundunar yan sanda a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu tayi kira ga al’umman jihar Yobe da su kwantar da hankulansu, su kuma cigaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullun ba tare da tsoro ba.

Kakakin rundunar yan sanda, reshen Yobe, Abdulmalik Abdulhafeez, ya bayyana kiran a jawabin da ya biyo bayan tsare hare-haren da yan ta’addan Boko Haram suka yi yunkurin kaiwa Damaturu, babbar birnin jihar.

Boko Haram: Rundunar yan sanda ta ba mutaneen Yobe tabbacin samun kariya

Boko Haram: Rundunar yan sanda ta ba mutaneen Yobe tabbacin samun kariya
Source: UGC

“Muna sanar da al’umma cewa kada su tayar da hankali akan al’amarin.

“Rundunar yan sanda da na soji da sauran hukumomin tsaro na iya bakin kokarinsu don ganin ba a samu barazana ga zaman lafiya da doka ba."

KU KARANTA KUMA: An kama dan sandan da aka gano a bidiyo yana cin zarafin wani dalibin Delta

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa rundunar soji tayi nasara a aikin Sector 2, Operation LAFIYA DOLE wanda yayi sanadiyar dakile hare-haren da yan ta’addan Boko Haram suka yi yunkurin kaiwa Damaturu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel