Saboda harin'yan ta'adda: Al'ummar Zamfara za su samu tallafin N10bn na jin-kai

Saboda harin'yan ta'adda: Al'ummar Zamfara za su samu tallafin N10bn na jin-kai

- Majalisar dattijai ta amince da ware N10bn a kasafin kudin 2019 a matsayin kudin jin-kai domin tallafawa wadanda rikicin 'yan ta'adda a jihar Zamfara ya dai-daita su

- Haka zalika majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta kafa wani kwamitin jin-kai ga al'ummar jihar Zamfara mai suna PIZAMS, domin alkinta kudaden

- Rahotanni sun bayyana cewa akalla mazaje 11,000 ne 'yan bindiga suka kashe a jihar, wanda ya bar akalla zawarawa 22,000 da kuma kiyascin marayu 44,000

Majalisar dattijai ta amince da ware N10bn a kasafin kudin 2019 a matsayin kudin jin-kai domin tallafawa wadanda rikicin 'yan ta'adda a jihar Zamfara ya dai-daita su, da kuma wadanda hare haren 'yan bindigar ya shafa a jihar.

Haka zalika majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta kafa wani kwamitin wucin gadi da za a kira shi da kwamitin jin-kai ga al'ummar jihar Zamfara na fadar shugaban kasa (PIZAMS), wanda zai shafe shekaru 10 domin alkinta kudaden da kuma tabbatar da cewa an raba tallafin yadda ya kamata.

A yayin da ta ke yin Allah-wadai kan hare haren 'yan bindigar da yayi sanadin mutuwar jama'a da dama a jihar, majalisar dattijan ta jinjinawa 'yan Nigeria, da suka ajiye banbance banbancen al'adu, addini ko kabilanci, suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin yin Allah-wadai da kuma nuna takaicinsu akan rikicin da 'yan uwansu na jihar Zamfara ke fuskanta.

KARANTA WANNAN: Da aringizon kuri'u ka samu nasara - Abba ya caccaki Ganduje kan ikirarin lashe zabe

Sanata Marafa

Sanata Marafa
Source: Depositphotos

Da ya ke gabatar da wannan kudurin gaban majalisar dattijan, Sanata Kabiru Garba Marafa (APC, Zamfara), mambobin majalisar dattijan sun koka kan yadda ake kashe 'yan Nigeria ba ji ba gani a fadin kasar.

Da ya ke jagorantar muhawara kan kudurin, Marafa ya ce ayyukan 'yan ta'adda, 'yan bindiga, barayin shanu da masu garkuwa da mutane a garuruwan jihar na ci gaba da ciwa jihar tuwo a kwarya.

Ya ce akalla mazaje 11,000 ne 'yan bindiga suka kashe a jihar, wanda ya bar akalla zawarawa 22,000 da kuma kiyascin marayu 44,000.

A jawabansu daban daban, mambobin majalisar sun bayyana cewa matsalar tsaro a kasar na ci gaba da zama babbar barazana, inda suka bayyana cewa ya zama wajibi gwamnati ta tashi tsaye haikan domin kare rayukan 'yan Nigeria.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel