Atiku a take-taken sa zai kawo rudani da rashin zaman lafiya a Najeriya - Lauretta Onochie

Atiku a take-taken sa zai kawo rudani da rashin zaman lafiya a Najeriya - Lauretta Onochie

Hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta zaurukan sada zumunta, Misis Lauretta Onochie, ta bi sahun jam'iyya mai ci ta APC wajen zargin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da yunkurin haifar da rudani a Najeriya.

Misis Lauretta Onochie, hadima shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan dandalan sada zumunta, ta zargi dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da kulle-kullen haifar da rudani da koma bayan zaman lafiya a kasar nan.

Atiku a take-taken sa zai kawo rudani da rashin zaman lafiya a Najeriya - Lauretta Onochie

Atiku a take-taken sa zai kawo rudani da rashin zaman lafiya a Najeriya - Lauretta Onochie
Source: Depositphotos

A makon da ya gabata Atiku ya fuskanci munanan zargi da suka hadar da cewa ya biya Dalar Amurka 30,000 ga wani dan kasar Amurka da ya shahara a kan cika-aiki domin tumbuke shugaban kasa Buhari daga kujerar sa.

An kuma zargi Atiku da cewa dan asalin kasar Kamaru ne sabanin yadda ya ke ikirarin asali da kasar Najeriya. Sai dai daya daga cikin hadiman sa tare da kungiyar sa ta yakin neman zabe sun yi watsi da wannan munanan zargi.

KARANTA KUMA: Kotun daukaka kara za ta yanke hukunci a kan Alkalin Alkalai Onnoghen

Cikin ababen zargi da hadimar shugaban kasa ta zayyana a shafin ta na sada zumunta, ta kalubalanci Atiku da yunkurin haifar da rudani yayin babban zabe wajen kulla tuggu ta mallake akwatunan zabe tun gabanin gudanar zaben.

Lauretta ta kuma zargi Atiku da neman hadin gwiwar dakataccen alkalin alkalai, Mai Shari'a Walter Onnoghen, wajen soke sakamakon zaben wasu jihohi 17 da shugaban kasa Buhari ke da rinjayen nasara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel