Kotun daukaka kara za ta yanke hukunci a kan Alkalin Alkalai Onnoghen

Kotun daukaka kara za ta yanke hukunci a kan Alkalin Alkalai Onnoghen

A yau ne Litinin, 15 ga watan Afrilun 2019, al'ummar Najeriya ke kirdadon shawara ta karshe da kotun daukaka kara za ta zartar na sanya ranar yanke hukunci a kan tsohon alkalin alkalai na Najeriya, Mai Shari'a Walter Onnoghen.

Rahotanni sun bayyana cewa, Mai Shari'a Walter Kanu Samuel Onnoghen, da ya kasance cikakken Alkalin Alkalai na Najeriya na 17, ya aike da wasikar ajiye aiki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 4 ga watan Afrilu.

Kotun daukaka kara za ta yanke hukunci a kan Alkalin Alkalai Onnoghen

Kotun daukaka kara za ta yanke hukunci a kan Alkalin Alkalai Onnoghen
Source: UGC

Ritayar Mista Onnoghen ta zo shekara guda da kuma watanni takwas gabanin lokacin da ya cancanci ya ajiye aiki da aka kayyade a watan Dasumba na shekarar 2020. Hakan zai yi daidai da shekarun sa 70 kuma ya dace da lokaci na barin aiki kamar yadda kotun koli ta shar'anta.

A halin yanzu Mista Onnoghen a ci gaba da fuskantar takaddama ta tuhumar sa da laifin rashin bayyana dukkanin dukiya da kuma kadara da ya mallaka bisa ga tanadi na dokoki da hukunce-hukunce na shari'a.

Kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito, a yau Litinin kotun tabbatar da da'a da ta kasance reshe na kotun kolin Najeriya, za ta yanke shawara a kan hukuncin da za ta zartar bayan shafe tsawon lokuta na sauraron karar masu korafi da kuma wanda ake tuhuma.

KARANTA KUMA: Farashin Man Fetur ya yi tashin doron zabuwa a jihar Bayelsa

Tarihi ya tabbatar da cewa, Onnoghen ya kasance zababben alkalin alkalai na Njaeriya yayin da Farfesa Yemi Osinbajo ya kasance mukaddashin shugaban kasa mai rike da akalar jagoranci, inda majalisar tarayya ta yi amanna da nadin sa a ranar 1 ga watan Maris kuma aka ranstsar da shi a ranar 7 ga watan Maris na shekarar 2017.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel