Buhari a take-taken sa Musulmi zai bari ya ci gajiyar kujerar sa - MASSOB

Buhari a take-taken sa Musulmi zai bari ya ci gajiyar kujerar sa - MASSOB

Kungiyar masu fafutikar neman assassa yankin Biyafara MASSOB, ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari a take-taken sa Musulmi zai ba gajiyar kujerar sa yayin kammala wa'adin sa a shekarar 2023.

Buhari a take-taken sa Musulmi zai bari ya ci gajiyar kujerar sa - MASSOB

Buhari a take-taken sa Musulmi zai bari ya ci gajiyar kujerar sa - MASSOB
Source: Depositphotos

Jagoran kungiyar MASSOB, Kwamared Uchenna Madu, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa a birnin Awka na jihar Anambra. Ya ce dukkanin wasu alamu sun bayyana cewa shugaba Buhari ya fara kulle-kullen tabbatar da wannan kudiri.

Kwamared Madu ya ce, alamu da take-taken shugaban kasa Buhari sun haskaka kudirin sa na ba Musulmin jam'iyyar APC dan kabilar Yarbawa gajiyar kujerar sa yayin da wa'adin sa a bisa kujerar jagorancin kasar nan ya kai gangara a 2023.

A yayin neman hukumar shari'ar kasar nan ta gaggauta dakatar da kudirin shugaban kasa Buhari, kungiyar MASSOB ta bayyana rashin jin dadi a kan yadda ya ke ci gaba da nadin Musulmai a matsayin shugabannin hukumomin tsaro na kasar nan.

KARANTA KUMA: Buhari ya nada sabon shugaban hukumar kwana-kwana na kasa

Kazalika kungiyar MASSOB ta ce dukkanin wasu alamu sun tabbatar da yadda kulle-kullen shuban kasa Buhari ke durkusar da wadanda ba su da akida ta Musulunci musamman yadda ya ba makiyaya na Fulani dama ta ci gaba da cin karen su ba bu babbaka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel