Buhari ya nada sabon shugaban hukumar kwana-kwana na kasa

Buhari ya nada sabon shugaban hukumar kwana-kwana na kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da amincewar sa ta nadin Mista Liman Ibrahim, a matsayin sabon shugaban hukumar kwana-kwana na kasa.

Babban sakataren hukumomin sasanta rikici a tsakanin al'umma ta Civil Defence, kwana-kwana, shige da fice da kuma gidajen yari, Al-Hassan Yakmut, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.

Buhari ya nada sabon shugaban hukumar kwana-kwana na kasa

Buhari ya nada sabon shugaban hukumar kwana-kwana na kasa
Source: Twitter

Yakmut cikin sanarwar da ya gabatar a garin Abuja, ya ce nadin mukamin sabon shugaban hukumar kwana-kwana na kasa zai fara tasiri ne tun daga ranar 29 ga watan Maris.

Babban Sakataren na hukumomin tsaro ya bayyana cewa, sabon nadin shugaban hukumar ta kwana-kwana ya biyo bayan ritayar tsohon shugaban hukumar, Mista Joseph Anebi.

KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin sabbin Jakadu 3 na Najeriya

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, bisa ga tanadi na dokokin aikin gwamnatin Najeriya, Mista Liman zai shafe wa'adi na tsawon shekaru hudu a sabon mukamin sa inda akwai yiwuwar tsawaita wa'adin sa duba da yadda hukunce-hukunce na kudin tsarin mulkin kasa ya shar'anta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel