Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin sabbin Jakadu 3 na Najeriya

Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin sabbin Jakadu 3 na Najeriya

Majalisar dattawa a ranar Alhamis, 11, ga watan Afrilu, ta tabbatar da nadin wasu sabbin jakadu uku da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi amincewar ta tun a farkon shekarar bana kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Shugaban Majalisar dattawa; Bukola Saraki

Shugaban Majalisar dattawa; Bukola Saraki
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tabbacin majalisar dattawa ya bayu ne a sakamakon rahoton bincike da tantance jakadu da kwamitin ta a kan harkokin kasashen ketare ya gudanar bisa jagorancin Sanata Monsurat Sunmonu.

Sababbin jakadun da majalisar ta tabbatar da nadin su sun hadar da Mista Christpher C. Chejina daga jihar Delta, Mista Bukar Kolo daga jihar Yobe da kuma Mista M.A Abdul daga jihar Benuwe.

Yayin gabatar da sakamakon binciken da kwamitin ya gudanar, Sanata Monsurat ta ce bayan tantance sabbin jakadun, majalisar ta yi na'am da cancantar su wajen wakilcin Najeriya a kasashen ketare ba tare da wani haufi ba.

KARANTA KUMA: Murnar samun nasara: Abba gida-gida ya yiwa Gwamna Ganduje raddi

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan jaridar Legit.ng ta ruwaito, majalisar dattawa ta yi amanna da nadin wasu sabbin jagorori na hukumar kididdiga ta kasa NBS, da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi tun a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel