Da aringizon kuri'u ka samu nasara - Abba ya caccaki Ganduje kan ikirarin lashe zabe

Da aringizon kuri'u ka samu nasara - Abba ya caccaki Ganduje kan ikirarin lashe zabe

- Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa sai da gwamnan jihar mai ci a yanzu ya tabka magudin zabe sannan ya samu nasarar cin zaben

- Ya yi kirarin cewa zaben na cike da sayen kuri'u, cin zarafin masu kad'a kuri'a, tauye 'yancin dan Adam da kuma tayar da fitintinu da dai sauransu

- A hannu daya shima gwamnan jihar ya zargi PDP da hada baki da rundunar 'yan sanda domin tabka magudin zabe a ranar 9 ga watan Maris

Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar PDP, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa sai da gwamnan jihar mai ci a yanzu kuma dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC ya tabka magudin zabe sannan ya samu nasarar cin zaben.

Injiniya Yusuf, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Laraba ta bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya ce tunanin Ganduje a yanzu bai wuce ya dauki hutu domin murnar abunda ya faru a ranar 23 ga watan Maris ba, zaben da a cewarsa bai cika sahihin ba.

KARANTA WANNAN: Duniya labari: Kudan Zuma ta kai hari Legas, ta kashe jami'in Kwastam yana aiki

Ya yi kirarin cewa zaben na cike da sayen kuri'u, cin zarafin masu kad'a kuri'a, tauye 'yancin dan Adam da kuma tayar da fitintinu da dai sauransu.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa, gwamnan jihar Kano, Ganduje, ya yi tsokaci kan zaben jihar da kuma zargin jam'iyyar adawa ta PDP da hada baki da rundunar 'yan sanda domin tabka magudin zabe a ranar 9 ga watan Maris, tun kafin daga bisani hukumar INEC ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammalaba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel