An saki yaron dan siyasa da akayi garkuwa da shi bayan biyan kudin fansa

An saki yaron dan siyasa da akayi garkuwa da shi bayan biyan kudin fansa

Masu garkuwa da mutane sun sako Yusuf Musa Sokodabo, dan babban dan siyasa a mazabar Abaji da ke Abuja bayan an biya su Naira Miliyan 1.2 a matsayin kudin fansa.

An sace Yusuf ne a safiyar ranar Lahadi a gidansa da ke Naharati.

Daya daga cikin iyalan Sokodabo da ya bukaci a boye sunansa ya shaidawa Daily Trust a jiya cewa an biya kudin fansan ne bayan an tattaunawa da masu garkuwa da mutanen da a farko suka ce sai an biya su Naira Miliyan 5.

DUBA WANNAN: An gwabza tsakanin leburori hausawa da matasa a Benin, mutum biyu sun jikkata

An saki yaron dan siyasa da akayi garkuwa da shi bayan biyan kudin fansa

An saki yaron dan siyasa da akayi garkuwa da shi bayan biyan kudin fansa
Source: UGC

Ya ce an saki Yusuf ne a wata daji da ke wajen garin Abaji inda jami'an sa kai suka mayar da shi gida.

Ya mika godiyarsa ga Allah bisa yadda dan uwansa ya dawo gida lafiya kuma ya bukaci gwamnati ta magance matsalar garkuwa da mutane a garin.

An yunkurin ji ta bakin Kakakin rundunar 'yan sanda na babban birnin tarayya, Abuja, ASP Danjuma Tanimu Gajere amma hakan bai yiwu ba saboda wayarsa ba ta shiga.

A makon da ya gaba, Legit.ng ta ruwaito muku cewa an aike da jarumin dan sanda Abba Kyari da tawagarsa zuwa hanyar Abuja zuwa Kaduna domin fattatar masu garkuwa da mutane da suke cin karensu babu babbaka a hanyar.

Yawaitan satar mutane a hanyar ya tilastawa mafi yawan matafiya Abuja da Kaduna komawa amfani da jirgin kasa domin kaucewa fada wa hannun miyagu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel