Kungiyar kwadago ta bawa Okorocha sati daya ya biya ma'aikatan jihar albashin da suke binshi

Kungiyar kwadago ta bawa Okorocha sati daya ya biya ma'aikatan jihar albashin da suke binshi

- Kungiyar kwadago takasa ta ba wa Gwamnan jihar Imo wa'adin kwanaki bakwai ya biya ma'aikatan jihar bashin albashin da suke binshi na watan Maris

- Kungiyar ta bukaci hakan ne bayan, gwamnan ya fito ya bayyana cewa babu wanda yake binshi bashin albashi a jihar

A jiya ne kungiyar kwadago ta jihar Imo ta bawa gwamnan jihar, Rochas Okorocha, kwanaki bakwai ya biya ma'aikatan jihar albashin watan Maris din da ya gabata.

Kungiyar ta ce ta na mamakin yadda aka yi ma'aikatan jihar har yanzu ba su karbi albashinsu na watan Maris ba, inda ta bayyana cewa akwai tabbacin an tura albashin ma'aikatan cikin asusun gwamnatin jihar.

Kungiyar kwadago ta bawa Okorocha sati daya ya biya ma'aikatan jihar albashin da suke binshi

Kungiyar kwadago ta bawa Okorocha sati daya ya biya ma'aikatan jihar albashin da suke binshi
Source: UGC

Bukatar kungiyar kwadagon ta zo ne bayan da gwamnan jihar Imo Rochas Okorochaya bayyana cewa ma'aikatan jiharsa ba sa binshi bashi, inda kuma ya bukaci ma'aikatan jihar su fito su fada idan akwai wanda ya ke binsa bashi.

Ma'aikatan sun bayyana cewa: "Ya mai girma gwamna, kungiyar kwadago ta jiha ta yi iya bakin kokarinta wurin ganin cewa an biya ma'aikata albashinsu na watan Maris, amma abin ya ci tura.

KU KARANTA: Dangote ya bayyanawa matasa hanyar da za su zama kamar shi

"Duk wasu dalilai da aka bayar na dalilin da yasa ba a biya ma'aikata hakkinsu ba, bai gamsar da ma'aikatan jihar ba. Bayan haka kuma sun bayyana cewa, kudin da ake warewa kananan hukumomi, da wasu kudade masu tarin yawa sun shiga asusun gwamnatin jihar. Saboda haka su har yanzu ba su san dalilin da yasa har yanzu ba a biya su albashi ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel