An kama dan sandan da aka gano a bidiyo yana cin zarafin wani dalibin Delta

An kama dan sandan da aka gano a bidiyo yana cin zarafin wani dalibin Delta

Kwamishinan yan sanda a jihar Delta ya tabbatar da kamun wani jami’in dan sanda wanda aka kama a faifan bidiyo yana cin zarafin wani dalibi.

A wani rubutu da aka wallafa a shafin twitter a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu ta shafin hukumar, rundnar yan sandan tayi Allah wadai da abunda jami’in nata yayi.

Hukumar yan sandan tace hakan ba koyarwar rundunar bane sannan cewa jami’in zai fuskanci shari’a.

Hukumar yan sandan tace: “Kwamishinan yan sandan jihar Delta ya tabbatar da cewa dan sandan da aka kawo rahoton cewa ya ci zarafi wani dalibi na tsare a hannun yan sanda.

“Hakazalika, za a fara shari’a sannan za a dauki matakin da ya kamata a kansa.

“Rundunar na burin sanar da cewa wannan hali ba koyarwar rundunar yan sandan Najeriya bace musamman a karkashin jagorancin mukaddashin Shugaban yan sanda, MA Adamu.”

KU KARANTA KUMA: Dole jama’a su daina dokar doka a hannun su inji Gwamna El-Rufai

Legit.ng ta ruwaito cewa rundunar yan sandan Najeriya ta sha caccaka na tsawon wani lokacin kan yadda jami’anta ke cn zarafin mutane da basu ji ba basu gani.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel