2019: Takarar Femi Gbajabiamila a Majalisar Wakilai tana rawa

2019: Takarar Femi Gbajabiamila a Majalisar Wakilai tana rawa

Watakila matsin lamba daga manyan ‘yan siyasa da kuma gwamnonin Arewa ta tsakiya na neman tilastawa jam’iyyar APC mai mulki ta ajiye goyon bayan da ta ba Femi Gbajabiamila a wajen shugabancin majalisar wakilai.

Da alamu APC tana tare da Honarabul Femi Gbajabiamila a matsayin wanda ta ke so ya rike majalisar wakilai. Sai dai yanzu gwamnonin da su ka fito daga shiyyar Arewa ta tsakiya sun shirya marawa wani ‘dan majalisar APC dabam baya.

Jaridar Vanguard ta kasar nan ta rahoto cewa Mutanen bangaren tsakiyar Arewacin Najeriya su na kukan ana nema ayi babu su a cikin gwamnatin Buhari don haka su ke shirin fito da wanda su ke so ya gaji Yakubu Dogara a majalisa.

Yanzu manyan ‘yan siyasan wannan yanki su na lissafin tsaida wanda za su ba goyon baya wajen takarar shugabancin majalisar wakilai a bana. Daga cikin wadanda ake sa rai akwai Mohammed Bago, Idris Wase da kuma John Dyegh.

KU KARANTA: Masu neman takara a APC na iya juyawa APC baya a zaben 2019

Tuni dai wasu gwamnoni na Yankin kasar sun fara nemawa ‘yan majalisun na su goyon baya domin ganin sun samu wannan kujera mai girma a Najeriya. Har ta kai Gwamnonin yankin su na neman goyon bayan 'yan siyasan wasu bangarori.

Ana rade-radin cewa shugaban APC ya zakulo Femi Gbajabilamila a matsayin wanda ya ke so ya rike majalisar wakilai a wannan karo, amma APC ta bakin Kakakin ta, Malam Lanre Issa-Onilu, ta karyata wannan magana a cikin makon nan.

Rahotanni na nuna cewa watakila APC tayi watsi da yankin Yarbawa ta fito da shugaban majalisar wakilai daga tsakiyar Arewa. Har yanzu dai shi Femi Gbajabiamila da mutanen sa ba su ce komai ba game da wannan tirka-tirika da ake yi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel