Gani ga wane: Fusatattun matasa sun kona wani dan fashi kurmus

Gani ga wane: Fusatattun matasa sun kona wani dan fashi kurmus

Jerin gwanon fusatattun matasa sun huce fushinsu akan wani dan fashi da makami da suka kama a garin Aba na jahar Abia, inda suka banka masa wuta ya kone kurmus bayan sun lakada masa dan banzan duka.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Yansandan jahar Abia, Mista Ene Okon ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Laraba, inda yace matasan sun kona dan fashin ne akan titin Umule dake cikin garin Aba.

KU KARANTA: Hansti leka gidan kowa: Kungiyar Izala ta shilla kasar Amurka don aikin Da’awah

Kwamishinan ya bayyana cewa matasan sun kama dan fashin ne lokacin daya raba hanya da sauran abokan satar nasa bayan sun kai ma wani kamfani dake unguwar hari, inda suka sace kayayyakin kamfanin.

Shima wani shaidan gani da ido ya tabbatar ma majiyarmu cewa bayan matasan sun kama dan fashin, sai suka daure masa hannuwa da wata katuwar sarka, sa’annan suka lakada masa dan banzan duka, bayan ya galabaita kuma suka watsa masa fetir suka banka masa wuta.

“Duk da halin da yake ciki yana ci da wuta, barawon ya tunjuma cikin wani kwata don ya kashe wutar dake cin jikinsa, amma matasan suka zakuloshi, suka kara watsa masa fetir, wanda hakan ya kara rura wutar dake cin jikinsa, haka jama’a suka cigaba da kallonsa har sai daya mutu.” Inji shi.

Sai dai kwamishinan Yansandan ya bayyana damuwarsa da wannan mataki da jama’an suka dauka, inda yace rundunar Yansanda ba zata lamunta ba, ya kara da cewa jama’a nada ikon kama barawo, amma basu da hurumin hukuntashi.

Daga karshe kwamishinan ya nemi jama’a su kauce ma daukan doka a hannunsu, kuma ya nemi su bashi hadin kai domin inganta tsaro a jahar Abia gaba daya, ta yadda rayukan jama’a da dukiyoyinsu zasu kasance cikin aminci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel