Tawagar lauyoyin APC sun shirya tsaf don kare nasarar Ganduje

Tawagar lauyoyin APC sun shirya tsaf don kare nasarar Ganduje

Tawagar lauyoyin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu sun nuna shirinsu don kare nasarawa Gwamna Abdullahi Ganduje.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa an kaddamar da Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben da aka sake a jihar a ranar 23 ga watan Maris.

Mista Ma’aruf Mohammed Yakasai, mamba kuma kakakin tawagar lauyoyin, ya sanar da matsayar APC yayinda yake jawabi a taron manema labarai a Kano a ranar Laraba.

Yace tawagar lauyoyin sun gano cewa akwai bukatar yin bayanin matsayarta domin mutunta rokon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda kotun zabe ta ba damar duba kayayyakin zabe da aka gudanar a jihar.

Tawagar lauyoyin APC sun shirya tsaf don kare nasarar Ganduje

Tawagar lauyoyin APC sun shirya tsaf don kare nasarar Ganduje
Source: Depositphotos

A cewarsa, tawagar lauyoyin sun shirya don kare nasarar Ganduje a gaban kotun zaben wacce ta fara zama a ranar Talata.

Ya ci gaba da cewa APC da Gwamna Ganduje sun shirya don kare kuri’un da mutanen jihar suka basu.

KU KARANTA KUMA: Dole jama’a su daina dokar doka a hannun su inji Gwamna El-Rufai

A cewarsa, dan takarar PDP, Abba Kabir-Yusuf bai da wani dalili da zai sa shi barazana ga nasarar Ganduje.

NAN ta ruwaito cewa shugaban kotun zaben, Justis Halima Shamaki a ranar Talata ta umurci INEC da ya bari PDP ta binciki kayan zaben da aka yi amfani dasu a zaben Gwamna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel