2019 Hajj: Birnin Tarayya ta fara taron wayar da kai ga maniyata

2019 Hajj: Birnin Tarayya ta fara taron wayar da kai ga maniyata

-Aliyu ya shawarci dukkanin maniyatan da su halarci wannan wayar da kai da za ayi kana kuma su kasance anyi komai da su da ya shafi wannan taron.

-Ya yi bayanin cewa wannan taro dai an rabashi zuwa sassa daban daban domin baiwa maniyatan damar sanin abinda aikin hajji ya kunsa

Hukumar kula da walwalar Alhazai ta Abuja zata fara gabatar da kashi na farko na wayar da kan maniyata wannan shekara a karshen makon nan.

Zance daga bakin kakakin kungiyar, Muhammad Lawal Aliyu, yace an riga da an tanadi malaman addinin musulunci domin wannan wayar da kai wanda za ayi a sansanin alhazan dake Basan Jiwa a Abuja a karshen makon nan.

Mahajjata

Mahajjata
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Da duminsa: Shugaban kasar Sudan ya yi murabus bayan shekaru 30 a kujerar mulki

Ya yi bayanin cewa wannan taro dai an rabashi zuwa sassa daban daban domin baiwa maniyatan damar sanin abinda aikin hajji ya kunsa da kuma wasu sabbin dokokin da hukumomin Saudiya da ta aikin hajjin kasa ta nan Najeriya (wato NAHCON) suka sanya a yanzu.

Aliyu ya shawarci dukkanin maniyatan da su halarci wannan wayar da kai da za ayi kana kuma su kasance anyi komai da su da ya shafi wannan taron.

Haka kuma ya roki maniyatan da basu dawo da takardarsu ta rejista ba ko kuma hoton shiga kasa da kasa da suyi saurin yin hakan domin ba hukamar tasu daman shirya takardunsu na tafiya.

Ya kuma sake shawartar maniyatan da suyi amfani da wannan dama wajen kara fahimtar ilimin addini musamman akan abinda ya shafi aikin hajji da kuma kasancewa akan tsari da addini ke so domin tsare martabar dukiyoyinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel