Dole jama’a su daina dokar doka a hannun su inji Gwamna El-Rufai

Dole jama’a su daina dokar doka a hannun su inji Gwamna El-Rufai

Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, yayi kira ga mutanensa da su guji amfani da rigima da tada rikici wajen nuna banbance. Gwamnan yayi wannan kira ne a Garin Kajuru.

Kamar yadda mu ka samu labari, Gwamnan Kaduna ya kai ziyara cikin karamar hukumar Kajuru bayan kashe-kashen da aka yi kwanan nan. Gwamnan yayi jawabi inda yace wadannan hare-hare ba za su kara komai ba sai bakin ciki.

Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana wannan ne a lokacin da ya shiga wani sansanin mutanen da si ka fake a Garin Marabar Kajuru, a Ranar Laraba 10 ga Watan Afrilu. Gwamnan ya nuna takaicin sa game da wannan mugun abu da ya faru.

Nasir El-Rufai ya kuma bayyanawa wadanda abin ya auka da su cewa, ya umarci hukuma da su yi kokari wajen ganin an maida su zuwa gidajensu. El-Rufai yace bai kamata mutane su ce sai sun rama irin ta’adin da aka yi masu ba.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun mamaye Yankin Katsina – Gwamna

Dole jama’a su daina dokar doka a hannun su inji Gwamna El-Rufai

Nasir El-Rufai lokacin da ya kai ziyara zuwa Garin Kajuru
Source: Depositphotos

Malam El-Rufai yake fadawa al’ummar Yankin na Kajuru cewa da zarar Fulani ko Mutanen Adara sun kai masu hari, abin da ya dace shi ne a fadawa jami’an tsaro domin su yi bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Gwamnan ya roki jama’a su daina daukar doka a hannun su domin tsaro ya smau Haka zalika gwamnan yace zai yi aiki hannu-da-hannu da jami’an tsaro da Sarakunan gargajiya da Malaman addini domin ganin tsaro ya wanzu.

Kwanan nan ne jami’an tsaro su ka tabbatar da cewa an kashe mutum 21, bayan an kuma sace shanu kusan 50 a cikin Garin Kajuru. Yanzu dai gwamnan jihar ya dauki duk matakan da su ka dace.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel