Matsalar jihar Zamfara ta fi karfin jami'an tsaro - Sanata Marafa

Matsalar jihar Zamfara ta fi karfin jami'an tsaro - Sanata Marafa

- Sanata Kabiru Marafa na jihar Zamfara, ya bukaci mutanen jihar da su zage dantse wurin kare kansu ta hanyar tallafawa jami'an tsaro, da gudummawar su wurin kare rayukan su da dukiyoyin su

- Sanatan ya bayyana cewa jami'an tsaron da ke jihar Zamfara ba su da yawan da za su iya kare al'ummar da suke samun barazanar 'yan ta'addar da ke jihar

Daya daga cikin Sanatocin jihar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa, ya bayyana cewa hukumomin tsaron Najeriya kawai ba su isa su magance matsalar tsaron da take damun jihar ta Zamfara ba.

A wata hira da ya yi da manema labarai, Sanatan ya bayyana cewa saboda ganin yadda 'yan ta'addar ke kashe jama'a, satar shanu, sannan kuma suke garkuwa da mutane don karbar kudin fansa, abin ya yi muni da yawa dole jama'a su fito su tallafawa jami'an tsaro wurin kawo karshen lamarin.

Matsalar jihar Zamfara ta fi karfin jami'an tsaro - Sanata Marafa

Matsalar jihar Zamfara ta fi karfin jami'an tsaro - Sanata Marafa
Source: Getty Images

Sanatan ya kara da cewa duk wani mutumi da zai fito ya bada labarin halin da al'ummar Zamfara su ke ciki, kawai zai fadi iya abinda ya ji ne, in dai ba wai ya je da kanshi ya ganewa idonshi ba.

Sanatan ya ce maza 'yan kalilan ne suke kwana a gidajensu idan dare ya yi.

KU KARANTA: An yi karon batta tsakanin 'yan ta'adda da 'yan kungiyar sa kai a Katsina

"Da ance maka an kammala sallar isha'i, abinda mazan yankin suke yi shine su shiga gida su dakko makamai, su fita su samu wuri su labe, ko akan bishiya, dutse ko wanni dan lungu dai da zasu iya gadin gidajensu."

Marafa ya kara da cewa, matakan da mutanen suke dauka ba wai yana nuni da cewa jami'an tsaro sun gaza ba, sai dai kawai jami'an tsaron basu da yawan da zasu iya kare garuruwan su daga 'yan ta'addar, saboda haka dole su fito su tallafa musu, wurin ba da tasu gudummawar, domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel