‘Dan takarar Sanatan PDP yana so a ba shi kujera a dalilin rikicin APC

‘Dan takarar Sanatan PDP yana so a ba shi kujera a dalilin rikicin APC

Wani babban kotun tarayya da ke zama a babban birnin tarayya Abuja, yayi fatali da karar da wani ‘dan takarar Sanata na jihar Bauchi shigar inda yake so a bayyana cewa shi ne ya lashe zaben da aka yi.

Garba Dahiru wanda yayi takarar kujerar Sanatan Kudancin jihar Bauchi ya nemi kotu ta tsaida shi a matsayin ainihin wanda ya lashe zaben da aka yi kwanaki, ganin cewa jam’iyyar APC da ta lashe zaben, ba ta da wani takamaimen ‘dan takara.

Jam’iyyar APC ta samu kuri’a 250, 725 ne a zaben Sanatan Bauchi ta Kudu, yayin da PDP mai adawa ta samu kuri’a 175, 527. Sai dai babu wanda aka iya ba takardar lashe zabe a dalilin rikicin cikin-gidan da ya barkowa jam’iyyar APC mai mulki.

Wannan ya sa Garba Dahiru wanda jam’iyyar sa ta zo na biyu a zaben, ya roki kotu ta bayyana shi a matsayin wanda yayi nasara a zaben na bana. Sai dai kotu ba tayi na’am da wannan roko ba inda tayi waje da karar sa a wani zama da aka yi.

KU KARANTA:

‘Dan takarar Sanatan PDP yana so a ba shi kujera a dalilin rikicin APC

Ana rikici tsakanin Lawal Gumau da Ibrahim Zailani a APC
Source: UGC

Kotun tarayya ta dauki wannan mataki ne a Ranar Laraba 10 ga Watan Afrilu. Har yanzu dai ba a ji hujjar da kotu ta bada na kin amincewa da rokon da ‘dan takarar na PDP ya kai gaban ta ba. Hakan dai zai ba APC damar kawo kujerar.

Idan ba a manta ba, Kotu tace APC ta canza sunan Lawal Gumau a matsayin ‘dan takarar ta na Sanatan Bauchi ta Kudu, sai dai jam’iyyar ba tayi hakan ba har lokaci ya kure. Wannan ya sa INEC ta gaza gane ‘dan takarar da ya ci zaben.

Lauyan hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta watau INEC, Alhassan Umar, ya ji dadin wannnan hukunci da kotu tayi. Sai dai Mai kare ‘Dan takarar PDP a Kotu watau Prisca Elesike, tace za su daukaka kara zuwa kotun gaba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel