Da duminsa: Shugaban kasar Sudan ya yi murabus bayan shekaru 30 a kujerar mulki

Da duminsa: Shugaban kasar Sudan ya yi murabus bayan shekaru 30 a kujerar mulki

Omar Al-Bashir, wanda rahotanni ke bayyanawa a matsayin mai tsattsauran ra'ayi kan siyasa da kuma shugabanci mai rikitaswa a kasar Sudan, ya yi murabus daga shugabancin kasar bayan kwashe shekaru 30 a kujerar mulki.

Wata kafar watsa labarai da ke daular larabawa (UAE) ta ruwaito cewa murabus din Mr Al-Bashir zai fara ne nan take. Shugaban kasar mai shekaru 75 ya mika mulkin kasar ga majalisar tsaro ta kasar da ke karkashin ikon rundunar soji.

Rahotanni kan murabus din Al-Bashir sun bayyana cewa awanni bayan da gidan talabijin mallakin kasar Audan ya ce akwai wani muhimmin sako da rundunar sojin kasar za ta gabatar kai tsaye a ranar Alhamis, amma dai ba ta yi karin haske kan sakon ba.

KARANTA WANNAN: Mulki da kudi: Saraki ya taya Aliko Dangote murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Da duminsa: Shugaban kasar Sudan ya yi murabus bayan shekaru 30 a kujerar mulki

Da duminsa: Shugaban kasar Sudan ya yi murabus bayan shekaru 30 a kujerar mulki
Source: UGC

Wannan murabus din nasa ya biyo bayan yawaitar zanga zanga da ake yi a fadin kasar, wacce ta zamo mafi girma a nahiyar Afrika, kuma murabus din Al-Bashir ya zo ne jim kadan bayan da sojoji suka mamaye fadarsa.

Dubunnan jama'ar garin Kharyoum suka yi zanga zanga a titunan babban birnin kasar na Sudan tare da yin tattaki zuwa shelkwatar rundunar tsaro ta kasar, inda suke zaune a bakin shelkwatar tun ranar Asabar da ta gabata. Akalla mutane 22 ne suka mutu a arangamarsu da jami'an tsaro.

Zanga zangar dai ta fara ne tun daga 19 ga watan Disamba, inda suke kalubalantar yadda gwamnatin Al-Bashir ke almundahana da kuma ruf-da-ciki da tattalin arzikin kasar, wanda ya tilasta karuwar farashin abinci, man fetur da kuma kudaden kasashen ketare.

Rahotanni dai sun bayyana cewa kotun sauraron manyan laifukan ta'addanci ta kasa-da-kasa ICC na neman Al-Bashir yanzu ruwa a jallo bisa zarginsa da aikata laifukan ta'addanci, ta'addancin da suka karya dokar dan Adam da kuma nuna wariyar launin fata da ke da alaka da Yammacin Darfur.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel