Amosun na shirin sallamar ma’aikatan MAPOLY

Amosun na shirin sallamar ma’aikatan MAPOLY

-Gwamnatin Amosun zata kori ma'aikatan kwalejin kimiyya da kere-kere ta Mashood Abiola daga aikin nasu

-A wani zancen kuwa daga bakin mai bawa Gwamnan shawara, ya karyata wannan maganar dake zagayawa a tsakanin makaranatar da ma jihar baki daya

Ma’aikatan Kwalejin kimiyya da kere-kere ta Moshood Abiola (wato MAPOLY) dake Abeokuta a jihar Ogun na zargin cewa Gwamna Ibikunle Amosun na yinkurin sallamarsu daga aiki.

A wani zance wanda Shugabannin wasu kungiyoyin makarantar suka sanyama hannu, yace Gwamna yana da yinkurin soke wadannan kungiyoyin guda uku wanda suka hada da; ASUP, NASU da SSANP tare da dukkanin kwamitinsu na zartarwa.

MAPOLY

MAPOLY
Source: UGC

KU KARANTA:Takaitaccen tarihin bakin Attajirin Duniya Aliko Dangote

Ma’aikatan sun kasance cikin wata tattaunawa da gwamnatin jihar akan mayar da MAPOLY zuwa jami’ar kimiyya da fasaha da kuma sake bude kwalejin kimiyya da kere-kere mallakar jihar a karamar hukumar Ipokia ta jihar Ogun.

Sun ce sauya kwalejin zuwa jami’a ba tare da an biya bashin albashin da ma’aikatan ke bin gwamnati ba tare da wasu hakkoki nasu wanda ya hada da fansho na naira miliyan 170 ya haifar da matsala tsakaninsu da gwamnatin.

Amma sai dai Rotimi Durojaiye, mai bawa Amosun shawara ya karyata wannan zargin yace sam ba gaskiya bane.

A wani labarin kamar wannan, Amosun ya nada sabbin manya sakatarori (Permanent Secreaty) goma sha takwas. Gwamna mai barin gado na jihar Ogun ya amince da nadin manyan sakatarori 18 cikin ma'aikantan jihar tasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel