Kwamitin Majalisa za ta soma bincike a kan Hukumar NBTE

Kwamitin Majalisa za ta soma bincike a kan Hukumar NBTE

Mun samu labari daga jaridar Daily Trust cewa ‘Yan Majalisar wakilan tarayya za su fara wani bincike na musamman a Hukumar NBET na kasa mai kula da saide-saiden wutar lantarki a Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan Majalisar kasar ta gano cewa hukumar ta NBET ta zabga asarar kudi har na Naira Biliyan 90. Yanzu dai kwamitin da ke lura da hakar wutar lantarki a majalisa zai fara gudanar da wannan bincike.

Wannan kwamiti na majalisa za ta binciki zargin da ke kan hukumar NBET na yin watsi da ka’idojin PPA na bada kwangila a Najeriya. Ana zargin wannan hukuma ne da sabawa dokoki wajen ba kamfanoni kwangiloli.

KU KARANTA: IMF ta ja kunnen Najeriya game da cin bashi a daga China

‘Dan majalisa Honarabul Mohammed Soba mai wakiltar yankin Soba ta jihar Kaduna a karkashin PDP, shi ne ya kawo maganar a gaban majalisar wakilai, inda yace idan su ka kyale hakan ya daure, an kafa mummunan tarihi.

Soba yake cewa mafi yawan kamfanonin da hukumar tayi aiki da su, ba a san da zaman su a Najeriya ba, sannan yace wannan hukuma ta NBET ta yi aiki da Azinge & Azinge law firms duk da cewa ba su cika sharudan aiki ba.

Majalisar tace akwai bukatar a binciki wannan lamari domin ganin gwamnatin Najeriya ta daina tafka asara. A 2010 ne gwamnatin tarayya ta kafa hukumar NBET domin ta shiga cikin masu lura da harkar wutar lantarki a kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel