Yan bindiga sun halaka mutane 18 tare da barnata dimbin dukiya a Katsina

Yan bindiga sun halaka mutane 18 tare da barnata dimbin dukiya a Katsina

Ashe dai har yanzu tsuguni bata kare ba, wai an sayar da biri an sayo kare, a yayin da jama’an jahar Zamfara ke samun saukin hare haren yan bindiga sakamakon tashi tsaye da jami’an tsaro suka yi, jama’an jahar Katsina kuwa kokawa suke yi game da halin rashin tsaron da suke ciki.

Anan wasu gungun mahara yan bindiga ne suka yi karamar hukumar Sabuwa ta jahar Katsina tsinke, inda suka kashe akalla mutane goma sha takwas, suka raunata wasu da dama, tare da kona motoci, shaguna da gidajen jama’a.

KU KARANTA: Gungun fitinannun masu garkuwa da mutane sun fada komar Yansanda

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jahar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar harin, sai dai ya bayyana cewa mutane goma yan bindigan suka kashe, daga cikinsu akwai Civilian JTF guda 6, sai yan bindiga guda hudu.

Kaakaki Isah ya kara da cewa Yansanda sun samu nasarar kwato kwashe gawarwakin Sojojin sa kai na civilian JTF guda shida daga cikin goma da yan bindigan suka kashe a yayin karanbattan da suka yi.

Wani shaidan gani da ido, kuma mazaunin garin Sabuwa yace da misalin karfe 4 na asubah na ranar Talata yan bindigan suka far ma garin Sabuwa sanye da kayan Sojoji dauke da bindigu kirar AK 47 da adduna iri iri.

“Suna shigowa suka fara harbin mai kan uwa da wabi, daga nan jama’a kowa yayi ta kansa muka afka cikin daji, idan baka yi bani wuri, sun kashe mutane goma sha takwas, sun kuma jikkata wasu da dama.

“Amma Yansanda basu zo ba har sai da yan bindigan suka gama cin karensu babu babbaka suka koma cikin daji, kuma a maimakon su bi sawunsu zuwa cikin dajin, sai suka koma ofishinsu.” Inji shi.

Daga karshe majiyar namu ya roki jami’an Yansanda da sauran hukumomin tsaro dasu taimaka ma al’ummar garin Sabuwa da karin jami’an da suke jibgewa a garin domin kare jama’a daga hare haren yan bindiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel