Tazarce: Ganduje ya kaddamar da kwamitin rantsarwasa mai mutane 100

Tazarce: Ganduje ya kaddamar da kwamitin rantsarwasa mai mutane 100

Zababben gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da kwamitin rantsarwarsa dake kunshe da mutane 100 da zasu kula da bikin rantsarwarsa da tsare tsaren sha’anin mulki zuwa ranar rantsarwa, 29 ga watan Mayu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu ne Gwamna Ganduje ya kaddamar da wannan kwamiti ne a fadar gwamnatin jahar Kano, inda yace babban aikin kwamitin shine tabbatar da tafiyar da gwamnatin Kano ba tare da wani tsaiko ba.

KU KARANTA: Gungun fitinannun masu garkuwa da mutane sun fada komar Yansanda

Tazarce: Ganduje ya kaddamar da kwamitin rantsarwasa mai mutane 100

Ganduje
Source: Facebook

Don haka gwamnan ya kara da bukatar kwamitin ta tabbatar da daura duk wasu aikace aikacenta akan nasarorin da gwamnatin ta samu, sa’annan yayi kira ga yayan kwamitin dasu taimaka mata wajen cimma manufarta.

A jawabinsa, shugaban jam’iyyar APC reshen jahar Kano, kuma sakataren kwamitin, Abdullahi Abbas ya tabbatar ma gwamnan cewa za’a gudanar da bikin rantsar dashi a ranar 29 ga watan Mayu cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.

Bugu da kari, Abdullahi Abbas ya bayyana ma jama’a cewa sai da aka duba cancanta kafin aka zabo mambobin kwamitin, don haka yace zasu yi aiki tukuru don mika rahotonsu cikin sati hudu, kamar yadda aka bukacesu.

Gwamna Ganduje ya daura alhakin jagorancin wannan kwamiti ne a wuyan sakataren gwamnatin jahar Kano, Usman Alhaji, tare da Alhaji Sano Nanono a matsayin mataimakin shugaban kwamitin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel