Wannan shine karona na farko, ban shiga da kafar dama ba - Mai garkuwa da mutane

Wannan shine karona na farko, ban shiga da kafar dama ba - Mai garkuwa da mutane

Wani matashi, Ismail Wakili, mai shekaru 19 da jami'an 'yan sanda suka cafke a Auga Akoko a jihar Ondo, bisa zarginsa da satar wani mutum mai suna Prince Omoghae Igbebon, ya ce wannan shine karonsa na farko a sana'ar garkuwa da mutane.

Wakili ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayar manema labarai a lokacin da rundunar 'yan sanda tayi bajakolinsa tare da ragowar wasu masu laifi su 15 ranar Laraba a Akure.

Matashin ya ce, su shida ne a cikin tawagar su ta satar mutane, ya bayyana sunayen ragowar biyar din da suka tsere kamar haka; Abdullahi Sanni (mai shekaru 33, dan asalin jihar Kogi), Mohammed Abdullahi (mai shekaru 36, dan asalin jihar Sokoto, Umoru Usman (mai shekaru 25, dan asalin jihar Kebbi) da Shehu Usman (mai shekaru 25, dan asalin jihar Neja).

Matashin ya amsa da bakinsa cewar tawagar su ce ke satar mutane tare da yin garkuwa da su a kan titin Akunnu Akoko zuwa Auga Okoko a jihar Ondo.

Wannan shine karona na farko, ban shiga da kafar dama ba - Mai garkuwa da mutane

'Yan sandan Najeriya
Source: Depositphotos

"Abdullahi ne ya saka ni a cikin wannan harka, ban shiga da kafar dama ba, don kuwa wannan shine karona na farko a cikin wannan sana'a

"Tunda na shiga kungiyar, wanna ne kadai mutumin da muka yi garkuwa da shi, na rantse ban taba aikata kisan rai ba, gaskiya nake fada," a cewar Wakili.

DUBA WANNAN: Buhari ya amince da kashe N1.3bn don biyan hakkin ma'aikatan da suka mutu

Sannan ya cigaba da cewa; "mun samu N70,000 a motar mutumin, bayan mun sace shi, daga cikin kudin ne Abdullahi ya ware N20,000 domin sayo mana kayan abincin da zamu ci tare da mutumin kafin a kawo mana kudin fansar sa.

"Ragowar N50,000 na tare da ni har zuwa lokacin da jama'a suka kama ni a garin Ibilo, a jihar Edo."

Kazalika, matashin ya bayyana cewar sun nemi N30m a matsayin kudin fansar mutumin da suka sace, amma daga bisani Abdullahi ya rage kudi zuwa N5m.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel