Rundunar yan sanda ta aika da jami’anta Arewa maso Yamma domin magance matsalolin tsaro

Rundunar yan sanda ta aika da jami’anta Arewa maso Yamma domin magance matsalolin tsaro

-Yan sanda a shirye suke tsaf domin shiga su fito da yan ta’addan a mafakarsu tare da masu garkuwa da mutane saboda yakarsu suke da shirin yi ba sassauci.

-Shugaban yan sandan ya kara da cewa rundunar tasu tayi nasarar cafke wadanda suka sace surukar Gwamna Aminu Masari kimanin wata daya da ya wuce.

Babban Sfeton yan sandan mai suna, Mohammed Adamu ya fadi hakan yace an tura kwarrarun jami’an yan sanda yankin Arewa maso Yamma domin magance matsalar dake addabar yankin ta garkuwa da mutane da kuma yan bindiga.

Adamu ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da Kungiyar da ke hulda da mutane wajen aikin da hada da yan sanda ranar Laraba a jihar Katsina.

Yan sanda

Yan sanda
Source: Twitter

KU KARANTA: Kuyi hankali da yankin Igbo, Ohanaeze ta gargadi masu satar shanu

Yace jami’an zasu kaiwa yan ta’adda farmaki ne a mazauninsu domin su tarwatsashi kana su kuma damke su tare da gaje mazaunin nasu ta yanda baza su dawo zuwa gareshi ba.

Adamu ya nemi goyon bayan jama’a ta hanyar sanar da rundunar yan sandan duk wani labari da zai iya taimaka mata wajen kawo karshen wannan al’amari domin cigaba da kare dukiyoyi da kuma rayukan jama’a wanda hakkin yan sanda ne.

“Yan sanda a shirye suke tsaf domin shiga su fito da yan ta’addar a mafakarsu tare da masu garkuwa da mutane saboda yakarsu suke da shirin yi ba sassauci.

“Sai ku taimaka ma yan sanda da duk wani bayani akan masu laifin a wuraren da kuke zama”.

Shugaban yan sandan ya kara da cewa rundunar tasu tayi nasarar cafke wadanda suka sace surukar Gwamna Aminu Masari kimanin wata daya da ya wuce.

“Babu wanda zai aikata laifi kuma ya kasance an kyaleshi,” yace.

Adamu, a karshe ya nemi malaman addini da su cigaba addu’o’in samun zaman lafiya da kuma na neman nasarar bisa ga kokarin da ita hukumar yan sanda keyi akan kawo karshe wannan matsalar dake addabar jama’a.

Yace ko shakka babu yin hakan zai taimaka wa yan sanda kwarai da gaske domin su cigaba da bada kariya ga rayuka da kuma dukiyoyin jama’a kamar yanda suka saba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel